
Sign up to save your podcasts
Or


A wannan mako, shirin ya yi duba ne a kan sabuwar hanyar koyarwa, da kuma tasirin da ta ke da shi a harkar ilimi a faɗin duniya, wato Innovative Teaching Method a turance.
Ita dai sabuwar hanyar koyarwa wato Innovative Teaching Method, hanya ce da ta sha bambam da hanyoyin koyarwa da aka saba gani a lokutan baya, domin ita ana koyar da ɗalibai ne bisa doron buƙatarsu ta koyo, ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da kuma na’urori, batare da malami ya zama shi ne ruwa kuma shi ne langa ba.
A wannan mako, shirin ya mayar da hankali ne a kan yadda tsarin jaddawalin karatun Najeriya ke haifar da koma-baya a fannin ilimin kasar.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha tsantsa hadi da lissafi, wato STEM Education a turance. Mafi yawancin kasashen Duniya da suka ci gaba, na bawa wannan tsari na Ilimin Kimiyya da fasaha tsantsa hadi da Lissafi fifiko a makarantunsu, la’akhari da yadda kimiyya da fasaha a wannan zamani suka zama ginshinkin ci gaba a sararin wannan duniyar.
Kuna iya latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake ci gaba da samun ci gaba a bangaren daliban da ke zuwa makaranta a yankin Arewacin Najeriya. Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adu'a da ke jihar Katsina ta samu nasarar yaye sama da dalibai dubu 10 a wannan shekarar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin ta re da Abdulkadir Haladu Kiyawa........
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan yadda aka fara mayar dahankali a kan karatun koyon sana'a a Kwalejoji da Jami'o'i a Najeriya.
Kuna iya Latsa alamar sauti domin sauraron shirin...
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda Dalibai a kasashen da suka ci gaba ke bayar da gudunmawa wajen sarrafa sinadarin "Hydrogene" da baya gurbata muhalli sosai, ta fuska kere-kere da nufin inganta iskar da ake shaka, bisa tallafin gwamnatocin kasashensu.
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako zai duba yadda matasa suka dukufa wajen amfani da yanar gizo don dogaro da kai.
Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya duba yadda mallakar takardun kammala karatu na bogi a Najeriya ke barzana ga karewar kwararru a fannoni da dama.
Ana fargabar idan har wannan dabi'a ta ci gaba a haka, tabbas za'a rasa kwararru musamman a fannin lafiya, kimiyya da sauransu.
Danna Alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni.
Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........
Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.
From the publisher's feed
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners