
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya yi duba ne da yada dalibai ke faduwa a jarabawar da ake yi da na'urar komfuta, wato CBT exams. Dallibai dai na yawan kokawa a kaan yadda sukaa faduwa sosai a irin wannan jarabawa, sabanin wadda suka saba, ta alkalami da takarda. Hasali ma daliban naa gaanin cewa matsalar ba daga gare su take ba, inda suka kawo dalilai da dama da ke nnuna cewa ba su daa laifi don sun fadi irin wannan jarabawar.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon ya mayar da hankali ne kan taron kungiyar malaman jami'o'in shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Makasudin wannan taro kamar yadda kungiyar ta bayyana shine nazari kan irin ci gaban da aka samu ko akasinsa a jam'i'o'in shiyyar da zummar lalubo hanyoyin samun mafita.
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda masu satar waya suka addabi al'ummar jihar Kano, da ke arewacin Najeriya.
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi nazarari ne kan cire tallafin mai da sabuwar gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi, inda a lokacin da ya ke gabatar da jawabi jim kadan bayan rantsar da shi, Tinubu ya sanar da janye biyan kudin tallafin mai da gwamnatin kasar ke yi, lamarin da ya sa farashin makamashin ya yi tashin gwauron zabi, kuma ya haifar da karin matsin rayuwa a kasar musamman a bangaren marasa karfi.
Iyaye da daliban abin ya shafe su, ganin yadda matakin ya tilasta wasu iyaye fara tunanin sauyawa 'ya'yansu makaranta sabida kasa iya ci gaba da biyan kudin motar da ake kai su makaranta don neman ilimi, a dayan bangaren ma, al'amarin ya shafi su kansu malaman makartu tun daga matakin Firamari da Sakandari da ma manyan makarantu.
Ku latsa alamar sauti donjin cikakken shirin..........
Shirin wannan mako dai ya yi nazari ne kan fasahar nan ta na'urar da ake sanya wa tunanin dan adam wato Artificial Intelligence, wadda a yanzu hankalin kasashen duniya ya fi karkata akai ganin yadda ya zo da gagarumin sauyi mai ban mamaki.
Sai dai duk da ci gaban da wannan fasahar ta zo da shi da ma wanda ake hasashen za ta samar nan da shekaru kadan masu zuwa, hankalin kasashen duniya ya rabu gida biyu wurin ci gaba da amincewa da wannan fasaha.
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna na wannan mako ya ci gaba ne akan na makon jiya wanda ya mayar da hankali kan tasirin koyarwa ta yanar gizo ko kuma E-Learning, a Turance.
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan tsarin ilimi ta yanar gizo ko kuma na shafukan Intanet da ake kira da E-Learning ko kuma Digilal Learning.
Tun bayan bullar cutar covid-19 ne dalibai da dama suka koma karatu ta yanar gizo ko kuma E-Learning a wani yunkuri na kaucewa ganin karatunsu bai gamu da tangarda ba.
A cikin wannan shirin za ku ji tasirin irin wannan karatu da kuma tagomashin sa ga daliban Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...........
From the publisher's feed
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners