Ilimi Hasken Rayuwa

Ilimi Hasken Rayuwa

By RFI HausaEducation
Download on the App Store

Ilimi Hasken Rayuwa episodes

  • Ƙalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar magana- Kashi na 2

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya ɗora ne akan shirin makon jiya sai dai a wannan karon shirin ya karakata ne ga ɓangaren yadda matasa ke sauya wasu kalmomin Hausa ta hanyar yi musu ƙawance da wasu yaruka su bayar da wata kalma da za ta bayar da ma'anar da za a fahimci abin da ake nufi cikin sauƙi.

    Idan mai sauraro na biye da shirin na Ilimi Hasken Rayuwa a makwannin baya-bayan nan yana ci gaba da bibiyar dokoki ko kuma ladubban rubutu da karatu baya ga magana da harshen na Hausa, harshen da ake ci gaba da ganin bunƙasarsa ba kaɗai a nahiyar Afrika ba, harma da sauran nahiyoyi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Kalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - kashi na 2

    Shirin na yau, ya ɗora ne akan kashi na farko da muka gabatar a makon jiya, wanda ya yi duba game da yadda harshen Hausa ya bunkasa a lokutan baya, da muhimmacinsa, baya ga matsalolin da yake fuskanta da ma kalubalen da Rubutun Hausa ke fuskanta a kafofin sada zumunta. 

    Masana sun bayyana ka'idojin rubutun Hausa, a matsayin wani yanayi na lura tare da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai ba tare da dungushe ko sauya ma'anar da marubuci ke nufi ba. 

    A cewar masanan kiyaye ƙa'idodin rubutun yana kuma samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.

    Ko da a kafafen yada labarai, rashin kiyaye ka'idojin rubutun Hausa yakan taka rawa wajen sauya ma'anar labari, to ko ya masu bibiyar shafukan  yanar gizo na kafafen watsa labarai ke ji idan suka ga ba a yi amfani da harufa masu lanƙwasa ba kamar Ɓ da Ɗ da kuma Ƙ? Ga abinda wasu ke cewa. 

    10 min
  • Ƙalubalen da suka dabibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - Kashi na 1

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon shirin ya sauya salo zuwa mai dogon zango ta yadda zai tattauna da masu ruwa da tsaki a kan bunƙasar harshen Hausa da matsalolin da ya ke fuskanta da dalilan da suka haifar da matsalolin, da dai sauran muhimman batutuwa da suka shafi harshen na Hausa.

    Harshen Hausa, harshe ne da yake da tsohon tarihi wanda ya shafe ɗaruruwan shekaru ana magana da shi, wanda alƙaluma suka tabbatar da cewar zuwa yanzu miliyoyin mutane ne ke magana da harshen a sassan duniya.

    Wani rahoto da aka wallafa a shekarun baya bayan nan ya nuna cewar a halin yanzu Harshen Hausa ne Harshe na 11 da aka fi amfani da shi a duniya, zalika an yi ƙiyasin cewar mutane miliyan 150 ne ke magana da shi a sassan Duniya.

    Masana na kallon waɗaccan alƙaluma a matsayin dallilan da suka sanya harshen na Hausa yin shaharar ta kai ya yi gogayya da dukkanin manyan harsunan duniya, lura da yadda harshen ke da yalwar kalmomi da za a iya sarrafa su gami da bayyana kowanne irin tunani da su, walau a litattafai, kafofin yaɗa labarai da sauran hanyoyi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Yadda ɗalibai a Bauchi ke watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai

    Shirin wannan makon zai yi dubi ne akan yadda ɗalibai a jihar Bauchi ke yin watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai.

    Jihar Bauchi, ta yi ƙaurin suna a baya a matsayin wadda ke sahun gaba wajen yawan yaran da suka yi watsi da makarantunsu tare da rungumar harkar tonon ma’adinai don samun dogaro da kai.

    Dalili ke nan da fiye da rabin daliban wasu makarantun firamare a jihar, suka bar zuwa makaranta inda suka karkatar da hankali kan harka haƙon ma’adanan.

    11 min
  • Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin ɗaukar nauyin karatun ƴaƴa mata zuwa PHD

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan shirin da gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar, na ɗaukar nauyin karatun ‘ya’ya mata daga Firamaren har zuwa karatun Digirin Digirgir, shirin da  ta ce tana fatan zai zaburar da ƙarin mata da iyayensu wajen duƙufa neman ilimi, ba tare da fargabar fuskantar ƙalubale na rashin ƙarfi ta fuskar tattalin arziƙi ba.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman.........

    10 min
  • Gwamnatin Ghana na nazarin yiwuwar fara bayar da ilimin Sakandire kyauta

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin Ghana na fara bayar da ilimin Sakandire kyauta, kodayake an faro da sauraren ra'ayin jama'a kan wannan shiri wanda ma'aikatar ilimin ƙasar ta bijiro da shi.

    Bayanai sun ce baya ga bayar da ilimin kyauta, tsarin zai kuma kawo gyara a yanayin bayar da ilimi musamman a manyan makarantun ƙasar ta Ghana.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

    10 min
  • Yadda matasa a Najeriya suka ƙirƙiri injin da ke tsince tsakuwa daga Shinkafa

    A wannan makon, shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara ya mayar da hankali kan yadda wasu matasa suka ƙirƙiri wani nau'in inji da ke cire tsakuwa daga jikin shinkafa, wanda zai taimaka matuƙa wajen samar da tsaftatacciyar shinkafa.

    Kafin wannan hoɓɓosa daga matasan, akan shigo da irin injinan ne daga ƙasashe irin China don sauƙaƙawa Manoma.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Gwamnatin Najeriya ta ɗaga likafar Kwalejin Kimiyyan Lafiya ta Tsafe zuwa Jami'a

    Shirin “Ilimi Hasken Rayuwa” namu na wannan mako, ya  yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurin samar da sabuwar jami’a kimiyyan lafiya da fasaha ta tarayya wato Federal University of Health Science and Technology a garin Tsafe na Jihar Zamfara, bayan tsallake dukkan matakan majalisa dokokin ƙasar.

    Wannan saka nannu na shugaban ƙasar ya yi zai bada damar ƙara inganta harkan kiwon lafiya ta hanyar samar da kwararru.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........

    10 min
  • Matsin rayuwa na barazanar gurgunta karatun ƙananan yara a Najeriya

    Shirin ''Ilimi Hasken Rayuwa'' tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yadda halin matsin rayuwa ke yin tasiri a kan karatun yara ƙanana lamarin da ya sa kaso mai yawa daga cikinsu ba sa samun cikakkiyar fahimta a kan darussan da ake koya musu, saboda dalilai da dama masu alaka da matsin rayuwar.

    Baya ga batun ci a koshi dai, yanyayin da yara ƙanana ke tafiya makarantunsu a yanayin da ake ciki ma lamari ne da ya kamata a mayar da hankali akai, la’akari da cewar a wasu lokutan ɗan hakin da ka raina kan tsone maka ido.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    10 min

About Ilimi Hasken Rayuwa

From the publisher's feed

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken…

More shows like Ilimi Hasken Rayuwa

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners