Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna ne game da sabbin Jami’oin Tarayya a Najeriya da tsohuwar Gwamnatin Goodluck Jonathan ta samar a Jihohin Kebbi da Yobe da kuma Zamfara a wani mataki na ganin dukkanin Jihohin kasar sun mallaki Jami’ar Tarayya. Ko wane hali ne Jami’o'in ke ciki a yanzu bayan sauyin gwamnati da aka samu a Najeriya. Shirin ya kai ziyara Jami’ar Gusau a Jihar Zamfara tare da tattaunawa da babban Jami’in tafiyar da ayyukan Jami’ar Alhaji Ibrahim Bawa Kaura.