A karon farko Jamhuriyar Nijar ta gudanar da gasar kokuwar gargajiya ta makafi zalla , in da aka ajiye takobi da wasu kyautuka ga wanda ya yi nasarar zama zakara a kokuwar. Ko da dai an gudanar da gasar ne a matsayin gwaji kafin daukaka shi har ya kai ga wani mataki a kasar kamar dai yadda za ku ji karin bayani a cikin na duniyar wasanni tare da Abdoulaye Issa.