Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da wani bincike da wata kungiyar bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa da kasa ta gudanar, inda ta gano cewa Kwamfuta na dakushe hazakar yara a makarantun Firamare, Kana yaran da ba sa amfani da Kwamfuta wajan neman ilimi sun fi hazaka fiye da takwarorinsu masu amfani da Kwamfuta.