Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad na tattauna ne akan matsalar kwankwadon kwayoyin kara kuzari tsakanin 'yan wasa musamman masu guje-guje da tsalle-tsalle yayin da hukumomin da ke da ruwa da tsaki ke ci gaba da kokarin ganin sun kawar da matsalar baki daya a duniyar wasanni.