Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya dore ne kan na makon jiya, in da ya tattauna kan matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na haramta shigo da magungunan da ke dauke da sinadarin Codeine saboda yadda matasa suka dauki sinadarin a matsayin wani abin maye, lamarin da ke matukar gurbata rayuwar matasan kamar yadda za ku ji a cikin shirin.