Shirin lafiya jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya tattauna ne kan cutar shawara, wato zazzabin yellow fever wadda ta barke a wasu jihohin Najeriya 16. Yanzu haka gwamnatin kasar tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya sun dukufa wajen bayar da allurar riga-kafin cutar musamman a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.