Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan manyan wasannin da aka yi tsakanin Manchester United da Leceister City daa kuma Arsenal da Chelsea a gasar Premier ta Ingila, in da muka zanta da magoya bayan kungiyoyin jim kadan da kammala fafatawar ta ranar Asabar.