Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka - Chanjin yanayi


Listen Later

Chanjin yanayi ko dumamar sa, batu ne dake cigaba da haddasa zazzafar muhawara da musayar ra'ayi tsakanin masana da kwararraru,musamman kan illolin da wannan batun zai haifar a rayuwar bil adama a doron kasa. Tuni dai wani taron kasa-da-kasa a birnin Copenhegen na Denmark,yayi kasedi cewa dole kowacce kasa ta tanadi yadda zata tunkari wannan batu na chanji yanayi daya fara bayyana a ambaliyar ruwan sama da kuma karancin sa a wani bangare na duniya bisa wasu dalilai.
Sai dai kuma kamar yadda bincike ya nuna a Nigeria kamar sauran kasashe masu tasowa inda wannan matsala ta chanji yanayi tafi bayyana,galibin jama'a basu san wannan batu ba,balle ma suyi la'akarin yadda zasu bullo masa. Wannan jahilcin dake bayyana game da batun na chanjin yanayi,yasa al'umma na cigaba da gurbata muhalli ba tare da sanin illolin da wannan gurbatar ke haifarwa ba.
Watakila dai chunkoson abubuwan hawa a birane dake fitar da gubataccen iska/hayaki da kuma musamman sarar itatuwa a matsayin makamashi,sune kan gaba wajen haifar da matsalolin gusowar hamada,zaizayar kasa da kuma yanayin dake barazana ga tsirrai ko yabanya. Wadannan sune mayan kalubalen da galibin kasashe masu tasowa ke fuskanta,kalubalen samun makamashi mai sauki domin rage chi iyakar da kullu yaumin ake wa dazuzzuka wajen neman itace girki.
A yayin da hukumomi musamman a Nigeria ke dawainiyar binciken wasu hanyoyi na samun makamashi mafi sauki da arha,bincike ya nuna cewa sana'ar itace da yin gawayi,na cigaba da bunkasa a yawanci jihohi da kananan hukumomi duk kuwa da cewa akwai dokar dake tsawatawa kan haka.
...more
View all episodesView all episodes
Download on the App Store

Muhallinka RayuwarkaBy RFI Hausa


More shows like Muhallinka Rayuwarka

View all
Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners

Kida, Al'adu da Fina-Finai by RFI Hausa

Kida, Al'adu da Fina-Finai

1 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Mu Zagaya Duniya by RFI Hausa

Mu Zagaya Duniya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners