Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

By RFI Hausa
Download on the App Store

Muhallinka Rayuwarka episodes

  • Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka

    Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka.

    Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka hasarar akasarin amfanin gonar da aka shugka da wuri.

    19 min
  • Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani

    A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci.

    19 min
  • Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria

    Matsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu.

    Wannan matsala ba kawai ta tsaya kan iyalai da kan rasa ruwan amfanin yau da kullum a gidajensu ba, har ma tana shafar ingancin muhalli, kasancewar a kan muhallin a kan dawo, don neman ruwan a karshe.

    20 min
  • Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar

    Shirin muhallinka rayuwarka na wannan mako zai maida hankali ne kan yanda ake karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma don ita ce babbar hanyar dogaro da kai ta fuskar abinci.

    Tun bayan halin matsin da jama'ar Jamhuriyar Nijar suka shiga biyo bayan juyin milkin soja da ta haddasa karamcin da tsadar abinci a cikin kasar aka rika zaburar da mutane su kama aikin noma musamman abincin da aka shigo da shi daga ketare Wanda ba a nomawa a cikin kasar irinsu shinkafa. Aka dai ce da rashin tayin ake barin arha, ganin yanda gwamnati ta kyautata wuraren da za a iya aikin noma a sassan kasar daban daban, mutane da yawa sun fada noman kuma hakika kwalliya ta fara biyan kudin sabulu. 

    20 min
  • Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar

    A yau shirin zai leka jamhuriyar Nijar ne inda matasa daga kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada da zaizayewar kasa don mayar da yankin tsanwa suka kai rangadi a Nijar musaman a Jihohi 5 na kasar da suka hada da Tillaberi Niamey, Dosso, Maradi da Zinder don duba irin cigaban da Nijar ta samu a wannan fannin da nufin kwaikwayonsa don kaddamar da shi a kasashensu.

    19 min
  • Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana

    Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana.

    Bayanai daga ƙasar ta Nijar na cewa a halin da ake ciki, Manoma da dama sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda rashin samun kuɗaɗen shiga, la'akari da irin rawar da noman na Albasa ke taka wa wajen sama musu abin kashewa.

    20 min
  • Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona

    Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........

    21 min

About Muhallinka Rayuwarka

From the publisher's feed

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

More shows like Muhallinka Rayuwarka

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners