
Sign up to save your podcasts
Or


Tun a karshen watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki, wato shekarar 2025, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da shirin noman na yankin sahara karamar hukumar Maigatari dake masarautar Gumel.
A jawabin da ya gabatar a yayin kaddamar da shirin, gwamnan jihar, Umar Namadi ya ce an kirkiro shirin ne don bunkasa noma da samar da abinci da ayyukan yi da kuma rage kwararar mutane daga kauye zuwa birane.
Shirin Muhallinka Rayuwa na wannan mako yayi duba ne kan yadda ake ƙara samun ƙaruwar yin noman cikin gida musamman a yankin Arewacin Najeriya, yankin da hukumomi suka dade suna kiraye kiraye kan a rungumi harkar noman. Za mu kuma duba yadda hakan zai taimaka wa wadata ƙasa da abinci da kuma fa’idarsa ga muhalli.
A cikin shirin 'Muhalllinka Rayuwarka' na wannan makon, za mu yi duba ne akan yunkurin da gwamnatin jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya ke ta yi na habaƙa noma da sarrafa rogo. Mun ji daga mahukunta da manoman rogo a jihar, sai masana harkar noma da sauran masu ruwa da tsaki.
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin jihar Jigawa ta tarayyar Najeriya na gina sabbin ƙananan madatsun ruwa 10 a jihar domin bunƙasa harkar noman rani.
A wannan shirin za mu ƙarƙare jerin shirye-shiryen da muka fara kawo muku akan halin da madatsun ruwa ke ciki jihohin Kano da Jigawa a Tarayyar Najeriya, da kuma yadda ya haan ya shaf harkar noman rani da su, da kuma halin da ya jefa manoman da masunta, musamman ta fannin tattalin arzikinsu.
Cibiyar nazarin da bincike kan ƙasar noma ta jam'iar Bayero a jihar Kano dake Najeriya ce ta shirya taron da ya hada ƙasashe da masana da suka yi duba a kai.
Taron karo na biyar ya baiwa masana damar nazari don lalubo hanyoyin magance matsaloli da suka hadabi wannan sashe da ya hada da noma da kiwo a Sahel da wasu ƙasashen.
A wannan makon, shirin zai yi duba ne kan halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki, da irin amfanuwa ko akasi da masu cin moriyar su da suka haɗa da manoma da masunta da sauran al’ummmar yankunan ke yi da su.
Shirin namu na yau zai mayar da hankali ne akan yadda mahukunta a jihar Damagaram ko Zinder ta Jamhuriyar Nijar suka yi hobbasa wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa ga manoman da suka bada himma a bara, suka kuma ga amfaninta.
Shirin Muhalllinka Rayuwarka’ ya yada zango ne a jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar, inda ɗimbin manoman albasa suka shiga halin ‘ni ƴasu’ sakamakon yadda ƙaddara ta sa suka yi kiciɓis da mugun irin albasa, lamarin da ya sa suka tafka asara.
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwa da Gwamnatin jihar Jigawa ta yi da wani babban kamfanin samar da dabino na kasar Saudiyya da kuma wani kamfanin ƙwararru da bunkasa harkokin noma na Najeriya. Babbar manufar wannan haɗin gwiwar ita ce bunƙasa noman dabino a jihar, ta hanyar bullo da dabarun noma na zamani, da musayar fasahohi, da kuma samar da jarin noma.
From the publisher's feed
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners