
Sign up to save your podcasts
Or


A yau shirin zai yi nazari ne akan yadda karyewar farashin kayan abinci zai yi tasiri akan noman bana, sakamakon zargin da ake cewa gwamnatin ƙasar ta shigar da kayan abinci daga waje, wadanda ke gogayya da waɗanda manoman cikin gida suka noma. A shirin da ya gabata, mun kawo kukan da manoma ke yi akan wanna al’amari, inda suke cewa gwamnati ba ta yi wani abu a game da kayayyakin aikin gona da suke saya da tsada. A yau shirin zai duba irin tasirin da hakan zai yi da noman bana.
Manoma a Najeriya na cigaba da kokawa dangane da matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na karya farashin kayan gona a daidai lokacin da ƙasar ke ƙokarin samar da wadatar abinci.
Shirin ya yi duba kan yadda matsalar ta ƙaracin ruwa ke haifar da tasgaro a fannin noma don samar da wadatar abinci, inda mu ka ji daga manoma musamman na rani a Najeriya kan irin kalubale da su ke fuskanta na rashin samun wadataccen ruwa a gonakinsu, a daidai lokacin da ƙasar ta yi watsi da batun gyara galibin madatsun ruwa da ake da su ballantana ma a kai ga batun gina sabbi.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan makon tareda Micheal Kuduson wanda kashi na uku ne ya dora akan kashi na biyu wanda ya gabata a makon jiya. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata shirin ya mayar da hankali ne kacokam akan yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku, tafki, rafi ko kogi domin gudanar da harkokin noma da kuma kyautatawar muhalli.
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ci gaba ne daga shirin da kuka ji a makon jiya. Idan a wannan kashi na uku wanda shi ne na ƙarshe, ya mayar da hankali ne kan tasirin ruwan Tekuna da Tafkuna da kuma Koguna ga kyautatuwar muhalli ko gurbatarsa, da kuma hanyoyin magance ƙalubalen da muhalli ka iya fuskanta. Masana kimiyyar muhalli sun haƙiƙance cewa tabbas waɗannan nau'ika na ruwa guda uku suna da ɗumbin tasiri akan muhalli.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan bambancin da ke tsakanin teku da tafki da kuma kogi, tare kuma da yin duba game da irin gudunmowar da suke bayarwa ga muhall.
Babu shakka masana kimiyyar halittu sun kasa ita wannan duniyar da muke ciki zuwa ɓangarori guda hudu: na farko, wanda ke dauke da duk ragowar ukun shi ne tsandauri, wanda ya hada da duwatsu da tudu da kwari da kasa da kwazazzabai, wadanda ake takawa ake tafiya a ciki da sauran abubuwa da ake yi yau da kullum.
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓataccen sauti ga lafiyar halittu da muhalli wato Sound pollution a turance daga nan RFI.
Shirin ‘Muhalllinka Rayuwarka’ ya na dubi ne kan batutuwan da ke da nasaba da muhalli, sauyin yanayi, da kuma noma da kiwo, kuma duk mako ya ke zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci, tare da abokinku, Michael Kuduson.
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne a kan noman kango ko kuma noman filin bayan gida wato Backyard Farming or Green House Farming a turance.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan fitar da amfanin gona da aka noma a damunar bara da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce a ke yi sakamakon karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da su ka ce ya sanya su suma su ka tsunduma cikin masu ribibin sayen amfanin gonar, su na adanawa a rumbunansu domin maganin gobe.
A farkon makon watan Janairun wannan shekarar, a yayin ziyarar gaisuwar sabuwar shekara da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ka kai wa Shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi bayani tare da ƙarin haske a kan aniyar gwamnonin.
Sai dai kungiyar Manoman ƙasar wato AFAN, ta bakin kakakinta Muhammad Magaji, ta bayyana cewa ba sabon abu bane yadda ake fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje domin neman riba, amma ta ce ƴan kasuwa da ke sayen kayan a hannun manoman ne ke yin hakan ba manoman da kansu ba.
Kasancewar matakin da gwamnonin su ka ce sun fara ɗauka na sayen kayan abinci su na adanawa na da buƙatar fashin baƙi daga masana, mun tuntuɓi Malam Abubakar Lawal Kafinsoli na sashen nazarin noma a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina dangane yadda hakan zai taimaka wa manoma da kuma harkar noma a ƙasar, wanda ya ce wannan ba hanya ba ce mai bullewa ba, musamman ga talakawan kasar.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan mako tareda Michael Kuduson ya mayar da hankali ne kan tasirin rashin tsara birane da gine-gine a kan muhalli, da kuma dangantaka tsakanin rashin tsara gari da gurbatar Muhalli.
From the publisher's feed
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners