
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan yadda wata al’ada da ake kira ''a ci ba'' dadi da ke zama babbar matsala ga manoma yayin girbin albarkar noma, a cikin wannan shiri za ku ji yadda manoman ke kokawa da yadda wannan al'ada ke kassara su, a wani yanayi da matsi baya ga tsadar kayakin noma ke ci gaba da ta'azzara.
Jamhuriyar Nijar inda tsuntsaye irinsu Angulu da Mikiya da ake samu a mayanka da bayan gari, inda ake jefar da gawawwakin dabbobi a yanzu sun zama tarihi. Za mu duba dalilan ɓacewarsu.
Masana a faɗin duniya sun yi ittifakin cewa ɓacewar waɗannan tsuntsaye, musamman ungulu ba karamin koma baya ba ne ga lafiyar muhalli. Kafin mu tafi jihar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar, za mu ji ƙarin bayani a game da ungulu da mahimancinsa ga muhalli da lafiyar al’umma, da kuma dalilan da su ka sa su ke ɓacewa daga doron ƙasa, daga bakinmasanin namun daji da abin da ya shafi halayyarsu.
Yau shirin zai yada zango a ne a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda mamakon ruwan sama da aka yi a cikin kwanakin da suka gabata ya haddasa ambaliya, lamarin da ya jefa al’umar yankuna da dama cikin halin kaka-ni-ka yi. A bangaren da ya shafi noma kuwa, ambaliyar ta janyo wa manoma ɗimbin asara, wanda ana iya bayyana a matsayin mara misaltuwa, duba da irin halin da suka shiga.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ya mai da hankali ne a kan yadda wani zubin amfani da kayan gona musamman kayan marmari da a kan yi wa feshi ke haddasa matsalolin kamuwa da cututtuka masu lahani ga rayuwar bil'adama, har ma a iya samun rasa rayuka.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson....
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali ne kan irin gudunmawar da sarakunan gargajiya ke bai wa ɓangaren noma a Jamhuriyyar Nijar musamman a wannan lokaci da sauyin yanayi ke barazana ga harkokin na Noma.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan wata hadaka da aka samu tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma katafaren kamfanin nan na sarrafa amfanin gona a Najeriya Wato OLAM, domin farfado da tsarin aikin Malaman Gona ta hanyar horar da wadanda jihar ke da su tare da kara yawansu a kokarin da bangarorin biyu ke yi na shirya samun ninkin amfanin gonar da za a rinka nomawa a jihar ta Kwara.
Shirin wanan makon zai yi dubi ne kan yadda yawan sare itatuwa ke mummunan tasiri a kan muhalli, da aikin noma, inda muka ziyarci jihar Adamawa a Tarrayyar Najeriya .
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan mako zai yi dubi ne kan shirin gwamnatin Najeriya na ɓullo da tsarin biyan haraji kan masu gurbata muhalli ta wajen ayyukan da suke gudanarwa, wanda a turance ake kira carbon tax. Kuma ana sa ran wannan harajin zai tursasa wa masana’antu da ke gurbata muhalli yin takatsantsan.
Wannan sabon haraji dai har yanzu ba’a gama tantance jadawalin yadda za’a aiwatar da shi ba, amma kwararru a fannin na ta kira ga jama’a da su yi shirin rungumar sa, bayan da suka ce gwamnati na yin tsare-tsare ne don fito da kowa zai biya haraji daidai da yawan hayaƙi mai gurɓata muhalli da yake fitarwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Machael Kuduson.......
Allah ya halici wannan duniya tamu da koguna da dazuka wadanda ke taimako ga rayuwar dan Adam ta hanyoyi da dama.
A matakin Nigeria, Allah ya albarkace ta da manyan gandun dazuzzuka da suke da fadi da girma, wadanda suka kunshi nau’o’in tsirrai da mabanbantan dabbobi, wadanda ba a samun su a dazuzzukan da ke wasu yankunan duniya.
Amma wasu daga cikin irin wadannan dazuzzuka kamar Dajin Sambisa a jihar Borno, Dajin Falgore a jihar Kano, da kuma Dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna tare da Dajin Kuyambana a jihar Zamfara sai Dajin Zugurma a jihar Neja da kuma Dajin Lame – Burra a cikin jihar Bauchi, a baya sun kasance maboya ga miyagu.
Shirin wannan zai yi dubi ne kan wani rahoton da ya ce an samu hauhawar amfani da makamashi mai gurɓata muhalli da ma hayaƙin da ke illata muhallai a shekarar 2023. Shirin zai duba tasirin wannan al’amari ga muhalli da ma abin da ake buƙatar ɗan adam ya yi don ci gaba da harkokinsa a cikin wannan sarari na subahana
Wani rahoto a kan makamashi da cibiyar makamashi ta duniya ta fitar ya nuna cewa yawan makamashi mai gurɓata muhalli da aka yi amfani da shi, da kuma hayaƙi mai illa da aka fitar a shekarar 2023 ya kai ƙololuwar da ba a taɓa gani ba, duk kuwa da yadda aka rungumi makamashi mai sabantuwa, mara gurbata muhalli a sassa da dama na duniya.
From the publisher's feed
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners