
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Michael Kuduson ya tattauna ne akan muhimmancin kula da ƙasar noma ta yadda za ta amfanar da al’umma ta fuskar bunƙasar ayyukan noma.
A cikin shirin wannan makon, zamu ji cewa a karon farko, gwamantin tarayya Najeriya ta kaddamar da shirin noman rani da na damina a jihar Cross River a ƙoƙarin da ta ke yi na haɓɓaka noma don samar da isasshen abinci, kuma ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari ne ya kaddamar da shirin noman rani na farko a madadin gwamnatin tarayya a wannan jiha da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Najeriya na cikin kasashen da suka yi fice a noman rani dana damina, inda manoman ke noma shinkafa, tun bayan da tsohuwar gwamnatin ƙasar ta hana shigo da wasu nau’ikan kayan abinci, ciki har da shinkafa a wani ƙoƙari na bunƙasa noman shinkafar a cikin gida.
Shirin ya yada zango ne a Nassarawa dake tarayyar Najeriya, jihar da ta bayyana shirin shiga harkar noman shinkafa ita da kanta, inda ta ware kadada sama da dubu 10 don noma shinkafar.
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Michael Kuduson kamar kowanne mako a wannan karon ya yi duba ne kan tsarin noma mai ɗorewa da ke nufin magance matsalar ƙarancin abinci da kuma yadda za a baiwa muhalli kariya.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ya yi tattaki zuwa Kano, inda hadin gwiwar Bankin Duniya da Gwamnatin jihar, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki kan kiwon dabbobi, domin inganta fannin ta kyautatawa ko zamanantar da tsarin kiwon dabbobin, samar da abincinsu, da kula da Lafiyarsu, gami da sarrafa madara da naman da suke samarwa.
A yau shirin zai leka Jamhuriyar Nijar don duba matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo da ta jawo yaduwar sakaran gari ko tumbin jaki, wata kalar ciyawa dake mamaye filayen noma da kiwo, kuma dabbobi sam ba sa cin ta, haka ba ta da wani amfani da aka sani ga al’umma.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ da ke nazari kan abin da ya shafi muhallli, canjin yanayi, noma da kiwo, ya yi tattaki zuwa Kamaru, inda ya duba shirin tallafa wa manoma wajen noman dawa mai jure fari da kasa mara kyau.
Hukumar kula da samar da albarkatun gona a arewacin Kamaru IRAD ce ke jagorantar aiwatar da shirin na sake fasalin bunkasa noman dawa 'yar rani, wato moskowari.
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon zai mayar da hankali ne a kan matsalar karancin nama da aka shiga a sassa da dama na Najeriya, inda za mu je jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar don jin yadda ake ciki da kuma inda matsalar ta ke.
A yau Shirin zai mayar da hankali ne kan wani babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano dake arewacin Najeriya Karkashin kulawar bankin Musulunci da Gidaunaiyar Bill and Melinda da Gidaunaiyar sarki Salman Wanda kungiyar harkokin noma ta SASAKAWA Africa ke jagoranta.
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne akan yadda gwamnatin jihar Jigawa ta samar da cibiyoyin tafi da gidanka sama da 300, domin kula da lafiyar dabbobi.
Mahukuntan na Jigawa sun kuma samar da wuraren sarrafa nama da kuma madara, matakan da suka sun ɗauka domin bunƙasa harkar kiwo da zummar mayar da shi na zamani.
From the publisher's feed
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners