Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

By RFI Hausa
Download on the App Store

Muhallinka Rayuwarka episodes

  • An fara samun ci gaba a noman cocoa a Taraba

    ‘Muhallinka Rayuwarka, shiri ne da ke kawo batutuwan da suka suka shafi muhalli, noma da kiwo, matsalolinsu da kuma masalaha. Duk mako ya ke zuwa muku a wannan tashaa a kuma daidai wannan lokaci, abokinku ne, Michael Kuduson ke muku maraba lale da sauraro.

    Yau Shirin namu zai mayar da hankali ne a kan noman koko a tarayyan najeriya.

    20 min
  • Nigeria daya daga cikin kasashe masu noman auguda a nahiyar Afrika da duniya

    Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan noman auduga,

    a shekarun baya, Nigeria ta kasance daya daga cikin kasashe masu tinkaho da noman auguda a nahiyar Afrika da duniya baki daya.

    Sai dai hankalin mahukuntan kasar ya koma ga bangaren man petur bayanda Allah ya albarkaci kasar da mai.

    Jihohin da suka yi fice a noman auduga a kasar, sun hada da Zamfara, Katsina, Kano, Adamawa, Bauchi da kuma Gombe.

    18 min
  • Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta

    Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan  yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023  wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa  har zuwa wannan lokaci.

    20 min
  • Yadda tsananin zafi ya ci karo da lokacin azumin watan Ramadana

    Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka,  a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.

    Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.

    Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.

    21 min
  • Kaddamar da shirin inganta harkokin noma a jihar Niger

    Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare.

    A wannan aikin da aka kaddamar, gwamnatin jihar ta ce ta samar da kayan aikin fasahar noma na zamani tare da tanadar da dabarun noma daga kwararru.

    Ku latsa alamar sauti dn sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani.......

    21 min
  • Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika

    Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.

    Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.

    22 min
  • Shiri na musamman kan yadda bangaren noma ya fuskanci matsaloli a Najeriya

    Shirin "Muhallinka Rayuwarka"  a wannan mako na musamman ne, domin kuwa ya yi dubi ne a kan matsaloli da dama suka addabi bangaren noma a Najeriya, wanda ake ganin su suka hana kasar samarwa kanta abincin da zai wadata jama'arta musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar sa a kasuwanni.

    Shirin na dauke da rahotanni da kuma hirarraki daga sassa dagan daban na kasar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiruddeen Muhammad.....

    20 min
  • Yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta

    Shirin mu na wannan mako zai yi duba ne a kan batun yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta da ke tarayyar Najeriya  musamman a jahar Cross River.

    Wakilin mu dake yankin MURTALA ADAMU ya kai ziyara a wa ta Gona da ake wannan kiwon kuma ya zanta da wadanda suke sana'ar,  wa ta da ta rungumi sana'ar ta yi bayani dalla dalla yadda ake fara tsara kiwon da kuma abubuwa da suka dace a tanada.

    18 min

About Muhallinka Rayuwarka

From the publisher's feed

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

More shows like Muhallinka Rayuwarka

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners