
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan hasashen masana kan yiwuwar daukewar ruwan damuna da wuri a wasu sassan Najeriya, lamarin da zai haddasa gagarumar matsala a tsarin samar da abinci.
Wannan hasashe dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin samun kamfar abinci a sassan Najeriya musamman jihohin arewaci wadanda su ne ke samar da abinci ga kusan daukacin jihohin kasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin............
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan mako zai yi duba ne kan batun matsalar takin zamani da manoma ke fama da shi a Najeriya shekara da shekaru, duk da cewa tsadar takin na bana ba irin wadanda aka saba gani a baya bane.
Matsalar tsadar taki dai a yanzu ita ce ta fi ci wa manoma tuwo a kwarya a Najeriya.
A latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani...
A yau shirin zai bada hankali ne akan sakin ruwan madatsar ruwan lagdo da kamaru zata yi, wanda yanzu haka mazauna wasu yankuna da ruwan zai kwaranya ta cikin su a Najeriya ke cikin tashin hankali dangane da irin asarar kama daga ta rayuka har ya zuwa ta dukiyoyi.
A karshe dai, gwamnatin Nigeria, ta tabbatar da cewa makwabciyarta Kamaru, ta sako ruwan da ke tumbatsa daga cikin madatsar ruwan Lagdo, lamarin da kan kasancewa babbar barazana ga dunbin al’ummomin Nigeria.
A yau Shirin zai karkata ne a kan yadda mata ke taka muhimmiyar rawa a bangaren noma a Najeriya kuma kasancewar su a harkar noman na ba da gudunmawa ta bangrarori da dama.Manoma mata a tarayyar Nigeria, na taka rawar a zo a gani a fannin habaka samar da abinci don amfanin al’ummar kasar.
Shirin ya karkata ne akan wani shirin tallafawa manoma a Najeriya wanda Bankin raya Afirka ke tallafawa kan yadda za’a samu inganci da habakar samar da wadataccen abinci a fadin kasar wato agricultural transformation agenda support program karkashin ma’aikatar noma ta kasar wanda aka kaddamar a garin Bunkuren jihar Kano.
From the publisher's feed
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners