Muhallinka Rayuwarka

Muhallinka Rayuwarka

By RFI Hausa
Download on the App Store

Muhallinka Rayuwarka episodes

  • Halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya

    Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan batun halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya, tare da duba matakan da suke dauka na kare kai anan gaba.

    Idan ba a manta ba dai  Shekara guda kenan da faruwa mummunar ambiyar ruwa a wasu  jihohin Najeriya, kuma jihar jigawa dake arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar tayiwa barna

    21 min
  • Gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar amfani da noman alkama don samar da aikin yi

    A wannan mako shirin zai yi dubi ne akan shirin gwamnatin Najeriya na bunkasa noman alkama domin yaki da talauci da kuma wadata kasar da abinci.


    A wani mataki na kawar da matsalar zaman kashe wando da magance rashin aikin yi musamman tsakanin matasa, gwamnatin Nigeria ta kuduri aniyar amfani da noma wajen samar da guraben aikin yi wa dubban matasan da basa da abin yi a fadin kasar.
     

    20 min
  • Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya

    Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .

    Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karowandada suka kuma bayyana cewa anfi samun asarar mafi girma akan kayan lambu  amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba

    21 min
  • Hukumar hasashen yanayin Najeriya ta ce za a fuskanci bahagon yanayi a kasar

    Shirin wannan mako zai yi dubi ne yadda Hukumar da ke kula da harkokin hasashen yanayi ta Nigeria, ta yi hasashen samun wani gagarumin sauyin yanayi a yankunan arewa maso gabas da arewa ta tsakiya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Bugu da kari hukumar, ta bayyana cewa shima yankin kudancin Nigeria zai shiga yanayi na zafin rana da wasu alamun hadari, kana yankunan da ke kusa da ruwa, za su shiga yanayi na hazo da ganin alamun hadari.

    Jihohin kudancin Nigeria irin su Lagos, Delta, Rivers da Bayelsa, ana sa ran samun yanayin hadari da tsawa a wadannan kwanaki.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nasiru Sani ............

    21 min
  • Yadda manoman Najeriya suka tafka hasara a daminar bana

    A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan batun hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .

    Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karo, Ado Hassan yakasai shine mataimakin sakatare janar na kungiyar manoman shinkafa ta kasa RiFAN, reshen jihar Kano ya kuma bayyana cewa anfi samun hasarar mafi girma akan kayan lambu  amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba.

    20 min
  • Koma bayan da manoman Najeriya suka samu a kakkar girbi na Shekara ta 2023

    Shirin a wannan karo zaiyi dubi ne akan wasu bayanan kididdiga da suka yi nuni da cewa kakar noma ta shekara ta 2023, na daga cikin lokaci mafi muni ga mafi yawan manoman Nigeria a sakamakon matsalar sauyin yanayi da ta haifar da karancin ruwan sama.

    A halin yanzu dai, wata babbar kungiyar kasa da kasa mai suna Action Aid, ta bayyana cewa irin hasarar da manoman Nigeria suka dibga a bana ta haura Nera Trilion 3, a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci a kasar.

    20 min
  • Amurka da Norway za su tallafawa manoman Afirka da dala miliyan 70

    Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, a wannan mako ya yi dubi ne a kan gidauniyar kudade daya kai dalar amurka miliyan 70 da kasar Amurka da Norway zasu samar don inganta harkan noma a nahiyar Afrika.

    Kasashen biyu sun sanar da hakan ne a garin  New York na kasar Amurka inda sukace kowacce a cikin su zata bada dala miliyan talatin da biyar-biyar, inda kuma suka jaddada cewar yin hakan yazama wajibi ne sabo da barazanar yunwa da ke addabar wasu yankunan Afrika a sanadiyyar matsalolin tsaro ko sauyin yanayi.

    Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin......

    20 min
  • Yadda aka horas da manoma dabarun yaki da matsalar dumamar yanayi a Najeriya

    Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar albarkatun ruwa da Bankin Raya Afrika suka horar da manoman karkara dabarun noma na zamani, wanda za su taimaka wurin yaki da dumamar yanayi da a yanzu duniya ke fama da shi wato Climate Change a turance.Wannan horo da aka baiwa wadannan matasa karkashin shirin na hadin gwiwa da ake kira da PIDACC, ba wannan shi ne karon farko da aka fara gudanarwa ba.

    An dauki shekaru sama da goma ana yinsa a wasu kasashen Yammacin Afrika da zummar sauya rayuwar al'ummar kasashen da kogin Niger River Basin ya ratsa.

    Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin......

    20 min
  • Yadda 'yan kasuwa ke sayen kayan abinci domin jiran kazamar riba

    Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda 'yan kasuwa a Tarayyar Najeriya musamman arewacin kasar, ke shiga kasuwanni da makudan kudi domin saye kayayyakin abinci, su kuma boye domin jiran lokacin da kayan za su yi tsada a kasuwanni kafin su fara fitowa da su da zummar samun kazamar riba, ba tare da la'akari da matsanancin hali da talakawan kasar ke fama da shi ba.

    Ku danna alamar sauti don sauraren cikakken shirin wanda ya zanta da masu ruwa da tsaki......

    20 min
  • Yadda sauyin yanayi ke haddasa wutar daji da kafewar koguna sakamon tsananin zafi

    Shirin Muhallinka rauwarka tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan sauyin yanayi wanda ya haddasa tsananin zafin da yanzu haka ya addabi kasashe da dama musamman a yankunan Turai nahiyar Asiya da kuma Afrika wada tuni ya haddasa gagarumar illa ta hanyar kafar da tarin koguna a mabanbantan yankuna.

    A bana kadai an ga tarin gobarar daji a kusan dukkanin nahiyoyin 3 wanda ya kone fadin kadada mai tarin yawa, lamarin da ke barazana ga harkokin noma da kiwo dama lalacewar kasar shuka.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin............

    20 min

About Muhallinka Rayuwarka

From the publisher's feed

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

More shows like Muhallinka Rayuwarka

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners