Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan fitar da amfanin gona da aka noma a damunar bara da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce a ke yi sakamakon karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da su ka ce ya sanya su suma su ka tsunduma cikin masu ribibin sayen amfanin gonar, su na adanawa a rumbunansu domin maganin gobe.
A farkon makon watan Janairun wannan shekarar, a yayin ziyarar gaisuwar sabuwar shekara da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ka kai wa Shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi bayani tare da ƙarin haske a kan aniyar gwamnonin.
Sai dai kungiyar Manoman ƙasar wato AFAN, ta bakin kakakinta Muhammad Magaji, ta bayyana cewa ba sabon abu bane yadda ake fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje domin neman riba, amma ta ce ƴan kasuwa da ke sayen kayan a hannun manoman ne ke yin hakan ba manoman da kansu ba.
Kasancewar matakin da gwamnonin su ka ce sun fara ɗauka na sayen kayan abinci su na adanawa na da buƙatar fashin baƙi daga masana, mun tuntuɓi Malam Abubakar Lawal Kafinsoli na sashen nazarin noma a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina dangane yadda hakan zai taimaka wa manoma da kuma harkar noma a ƙasar, wanda ya ce wannan ba hanya ba ce mai bullewa ba, musamman ga talakawan kasar.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.