Shirin Duniyar Wasanni, yayi waiwaye kan kyautar Ballond'Or da Cristiano Ronaldo ya samu nasarar lashewa karo na hudu. Cikin shirin za'a ji muhawarar da aka tabka tsakanin magoya bayan Lionel Messi da ya taba lashe wannan kyauta sau 5 , da kuma bangaren magoya bayan mai rike da kambun kyautar a yanzu, wato Cristiano Ronaldo.