Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan jawadalin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar na gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha. A nahiyar Afrika, Najeriya da Kamaru da Algeria aka hada a rukunin B yayin da aka sanya Zambia ta zamo cikin ta hudunsu.