Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da dan wasan Masar mai taka leda a kungiyar Liverpool ta Ingila, Mohamed Salah da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar Afrika na shekarar 2017 a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a birnin Accra na Ghana.