Shirin mu zagaya duniya ya wannan makon tare da Ramatu Garna Baba ya tattauna batutuwa da dama amma ya bayar da fifiko kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeiya bayan hukumar kididdigar kasar ta sanar a hukumance cewa kasar na fama da koma-bayan tattalin arziki. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da jama'ar kasar ke kusan tsadar rayuwa.