Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya yi gamsasshen bayani akan tarihin gasar kwallon kafar nahiyar turai ta Europa da kuma yawan kungiyoyin da suke buga ta. Zalika shirin ya amsa tambayoyin da suka shafi tarihi na Sarauta a kasar Hausa da kuma kan sha'anin Diflomasiyya tsakanin manyan kasashen duniya.