Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba ya yi karin bayani kan wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ta hanyar tattaunawa da masana kan fannin da aka nemi sani a kansa. Daga cikin tambayoyin da aka amsa a wannan mako akwai Tarihin Jamal Kashoggi dan jaridar kuma dan asalin Saudiya da aka yiwa kisan gilla a ofishin jakadancin kasar ta Saudiya dake birnin Istanbul na Turkiya.