Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan mako tare da Micheal Kuduson ya kawo muku wasu daga cikin tambayoyi da wasu masu sauraron mu suka nemi karin bayani, ciki harda tarihin sarkin Lafiyar Baribari dake jihar Nasarawa a Najeriya, Alhaji Sidi Bage Mohammed. Sai kuma batun matsalar tattalin arzikin kasar Ghana.