Da dama dai daga cikin matasa na baya-bayan nan ba su da cikakkiyar masaniya game da wasan Langa, watakila ma wasu basu ma san shi ba baki daya.
Wasan Langa a jihar Kadunan Najeriya da ke arewacin Najeriya, wasan da masana ke cewa na fuskantar barazanar bacewa, saboda rashin ba shi tallafi ko kuma goyon bayan da ya dace.
Abdulrahamane Gambo ya yi tattaki zuwa Kaduna a cikin shirin Duniyar Wasanni.