Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan murabus din shugaban Kwamitin Shirya Wasannin Olympics na Tokyo 2020, Yoshiro Mori bayan ya furta kalaman kaskanci ga mata. Kazalika shirin ya yi nazari game da sake dage bikin wasanni na kasa a jihar Edo ta Najeriya.