‘Daya daga cikin wasannin gargajiya da suka samu karbuwa a wajen jama’a a Nigeriya shi ne wasan Langa.Babban abinda kan burge mutane tare da jan hankalinsu game da wasan na Langa shi ne yadda dan wasa kan rike kafarsa daya tare da gudu bisa kafarsa daya.Wasan Langa, ya samo asali ne daga irin wasannin da yara kan yi, kafin daga bisani wasan ya samu daukaka.
Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasannin ya duba mana yanayin wasar Langa.