A cikin wannan shirin tare da Hauwa Kabir za ku ji yadda ta tabo muhimman batutuwa a masana'antun shirya fina-finai na Kannywood Bollywood da kuma Nollywood, ayi saurare lafiya.
A cikin shirin Dandalin fasahar Fina-Finai,Hawa Kabir ta mayar da hankali ga rayuwar yan Fim a Najeriya da wasu kasashe da suka hada da India,musaman labarin da wasu mutane ke bayar na mutuwar yan wasan Fim.
A cikin shirin Dandalin fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin masu ruwa da tsaki a Duniyar Fim a Najeriya,wanda suka kuma bayyana mata irin manyan ayuka da suke yi domin raya sashen fim ,banda haka irin kalubalen da suke fuskanta,musaman wajen rubuta Fim.
A cikin shirinmu na wannan makon tare da Hauwa Kabir, za ku ji yadda shugabannin hadakar hukumar da ke kula da shirya fina-finan hausa a Najeriya ta yi nasarar sulhunta manyan Jaruman masana'antar wato Ali Nuhu da Adam A Zango.
Da alama sabuwar baraka ta barke tsakanin manyan Jamruman Kannywood bayan wasu kalamai da Jarumi Adam A Zango ya furta na cewa babu tarbiyya a cikin masana'antar, asha sauraro Lafiya.
Shirin a wannan karon ya mayar da hankali kan yadda 'yan wasan hausa a jihar Kaduna ta arewacin Najeriya ke fadi-tashin ganin sun kafa masana'antar shirya fina-finai ta Kadawood don kaucewa dogaro da Kannywood da ke Kano.
A cikin shirin dandalin Fina-finai Hawa Kabir ta duba irin kalubalen da masu shirya fina-finai ke fuskanta wajen shirya fina-finai a arewacin Najeriya,duk da cewa suna bukatar karin taimako daga hukumomin kasar.
Ta samu zantawa da wasu daga cikin masu ruwa tsaki a duniyar Fina-Finan Najeriya.
Haoua Kabir a cikin shirin dandalin fasahar fina-finai ta tattauna da wasu daga cikin masu shirya fina-finai a arewacin Najeriya,sun kuma yi mata bayani dangane da hanyoyin da ske amfani da su wajen rubuta fina-finai,shirya fim dama saka shi kasuwa.
Shirin dandalin fasahar fina-finai na wannan mako zai mayar da hankali zuwa rayuwar mawaka a Najeriya.
Hauwa Kabir ta samu tattaunawa da daya daga cikin mawakan hausa na Najeriya.
20 min
About Dandalin Fasahar Fina-finai
From the publisher's feed
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa…
wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.