Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan mako ya yi tattaki ne zuwa Jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda ya dubi a karo na biyu akan sabuwar makarantar koyar da sana'ar Fina- Finai wacce Gwamnan Jihar Dr. Rabiu Musa Kwankwanso ya bude domin taimakawa fannin shirin fim a Jihar, inda aka yi kiyasin sama da matasa 20,000 sana'ar ta sama ayyukan yi a jihar.