Wasanni

Wasanni

By RFI Hausa
Download on the App Store

Wasanni episodes

  • Gwamnatin Najeriya ta jingine shiga gasar kwallon kwando
    A makon da ya gabata ne gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da tawagar kwallon kwando ta kasar daga shiga wasannin kasa da kasa na tsawon shekaru 2 da zummar daidaita al'amura a hukumar kula da wasan kwallon kwando ta kasar da rikici ya wa dabaibayi. Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya duba batun jigine shiga gasar.
    11 min
  • Zakarun Turai: Liverpool da Real Madrid sun kai wasan karshe
    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako ya duba batun gasar kwallon kafa ta  zakarun nahiyar Turai, wadda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta Spain da Liverpool ta Ingila suka kai matakin wasan karshe, abin da nufin cewa kungiyoyin biyun za su barje gumi a wasan karshe na gasar. Shirin ya tattauna yadda wasannin kusa da karshe suka kaya  tare da sharhi a kan karon battan da za a yi a wasan karshe.
    10 min
  • Mummunar hamayya tsakanin magoya bayan Kano Pillars da Katsina United
    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi mana dubi ne a kan yadda hamayya ke ci gaba da zafafa tsakanin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da na Katsina United. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne aka ci Kano Pillars tara bayan da magoya bayanta suka lalata mata motar da ke daukar 'yan wasanta. Shirin ya tattauna da masana masu bibiyar wasannin kwallon kafa a Najeriya a kan dalilan da suka ta'azzara wannan mummunar hamayya da ya ke zama hadari ga harkar tamaula.
    11 min
  • Dalilan da suka hana Najeriya zuwa gasar kofin duniya
    Shirin 'Duniyar Wasanni' na wanna makon ya yi nazari ne a ka gazawar babbar tawagar kwallon kafar Najeriya wajen samun tikitin  zuwa gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar nan gaba a wannan shekarar. Najeriya dai ta fafata ne da Ghana a wajen neman wannan tikiti, kuma bayan tawagogin biyu sun buga canjarars a can kasar Ghana, tawagar Ghana ta biyo ta Najeriya har gida, a filin wasa na Moshood Abiola ta karbi wannan tikitin a haduwa ta biyu.
    10 min
  • Fafutukar Najeriya da Kamaru wajen neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya
    Shirin na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali ne game da fafutukar kasashen Najeriya da Ghana ta neman gurbi a gasar cin kofin duniya bayan canjaras din da suka yi babu kwallo a wasansu na makon jiya da ya gudana a birnin kumasi, dai dai lokacin da suke shirin haduwa a zagaye na biyu na wasan gobe talata a birnin Abuja na Najeriya.
    11 min
  • Matakin FIFA da UEFA na dakatar da Rasha daga wasannin kasa-da-kasa
    Shirin duniyar wasanni na wannan mako tare da Abdurrahman Gamabo Ahmad ya cigaba da tattaunawa ne akan kan matakin hukumomin kwallon kafar Duniya FIFA da UEFA na dakatar da Rasha daga harkokin wasannin kasa-da-kasa, saboda da mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine, yayin da abangare daya wasu kasashe sukace baza suyi wasa da kasar ta Rasha ba.
    11 min

About Wasanni

From the publisher's feed

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

More shows like Wasanni

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners