Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.... more
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 351 episodes available.
November 18, 2023Bayani a kan masu 'kujerar naki' a Majallisar Dinkin DuniyaShirin 'Tambaya Da Amsa' na wannan mako kaamar kowane mako, ya kawo muku tambayoyi ne da masu sauronmu suka aiko mana, inda ya samar da amsoshinsu daidai gwargwadon iko. Daga cikin tambayoyin da muka amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin yadda aka yi wasu kebabbun kasashe suka samu "kujerar naki' a Kwamitin Tsaro nna Majalisar Dinkin Duniya....more20minPlay
November 11, 2023Tambaya dangane da bayani a kan kisan kare dangin HolocaustTambaya daga Alhaji Haruna Kira da Umar Ladan Baturiya daga jihar Jigawa Najeriya. So suke a banbanta musu tsakanin ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga. Ko akwai dokar da ke hana amfani da karfi fiye da kima a kan irin wadannan masu aikata manyan laifuka?...more20minPlay
November 04, 2023Amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraron RFIMe ake nufi da karbar rance na biliyoyin daloli don tallafa wa naira kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yanzu ta yi. Mataki ne mai fa’ida? Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ ne ke zuwa ma mai sauraro daga sashen Hausa na Radio France Internationale RFI. Ana iya aiko da tambayar da ake da ita ta adireshinmu na imel a [email protected] ....more20minPlay
October 28, 2023Bayani a kan ramin mafi tsawo a duniya, wadda ke gabashin nahiyar Afrika ‘Tambaya Da Amsa’, daga sashen Hausa na Radio France Internationale, RFI, tare da abokin nan naku, Michael Kuduson.Shiri ne da ke kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, duk mako yake zuwa daga wannan tasha, kuma a lokaci irin wannan. Daga cikin tambayoyn da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan ramin nan mafi tsawo a duniya, wadda ke gabashin nahiyar Afrika, wato East African Rift....more20minPlay
October 21, 2023Karin bayani a kan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin DuniyaShirin yana zuwa muku ne da wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci. A cikin Shirin wannan makon, zai amsar tambayar da ke neman Karin bayani a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma gazawarsa da ma majalisar wajen kawar da yake yake a duniya,...more20minPlay
October 14, 2023Dalilan da suka haddasa barkewar yaki tsakanin Isra'ila da mayakan HamasShirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micael Kuduson, mayar da hankali kan neman karin bayani dangane da musabbabin sake barkewar rikici tsakanin kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu da Isra’ila. Akwai kuma wasu karin tambayoyin da shirin ya yi wa masu sauraro karin bayani akai....more21minPlay
September 30, 2023Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ya tabo batun cutar dake maida mutum zabayakamar yadda aka saba a ko wane mako shirin Tambaya da Amsa tare da Michael KJuduson, na mayar da hankali wajen amsa muhimman tambayoyin da kuka buka ci fita daga jahilcinsu. ina a wannan mako, shirin ya tabo batutuwa da dama, da suka hada da son sanin irin cutar dake kone fatar bakaken fata ta na zama farar sal....more20minPlay
September 23, 2023Tambaya da Amsa: Amsar tambaya kan alakar girgizar kasa da aman wutar dutseShirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko, kuma a wannan makon za ku ji ci gaban amsa kan dalilan da ke haddasa girgizar kasa dama dangantaka tsakanin wannan matsala da aman wutar dutse da kasashe da dama ke fama da su. Haka zalika akwai amsa game da tarihin Marigayi Malam Amadou mai wa'azi na jihar Damagaram a Jamhuriyyar Nijar wanda ya koma ga mahaliccinsa a ranar 3 ga watan Satumbar da muke ciki ya na da shekaru 73 a Duniya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin..............more20minPlay
September 16, 2023Fashin baki kan abin da ke haddasa girgizar kasa a duniyaKamar yadda muka saba a duk mako, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana kan duk wani abin da ya shige musu duhu....more20minPlay
September 09, 2023Fashin baki kan yawan juyin mulki a Yammacin AfirkaKamar yadda muka saba a duk mako, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana kan duk wani abin da ya shige musu duhu. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman fashin baki a kan yadda juye-juyen mulki suka yi wa yankunan Yammaci da Gabashin Afrika dabaibayi a baya bayan nan....more20minPlay
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 351 episodes available.