Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
September 11, 2020Wasanni - Wasannin dalibai na shekara-shekara a NijarA duk shekara dai ana hada daliban makarantu a Nijar don su fafata a wasannin shekara na dalibai don a fitar da zakaru tsakanin jahohin kasar ta Nijar.Ana shirya wannan kwambala dai ne mafi yawa a watan Maris a dai dai lokacin da dalibai ke zuwa karamin hutu ista ko paques.Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar....more11minPlay
September 07, 2020Wasanni - Tasirin cibiyoyin cacar zamani ga makalla wasannin kwallon kafa a Najeriya...more10minPlay
September 04, 2020Wasanni - Gasar tseren keke a NajeriaWasan tseren kekuna, na daya daga cikin tsofaffin wasanni a tarayyar Nigeria wanda aka faro a shekarar 1972 kuma sannu a hankali wasan ya habaka inda ya kasance wasan da kan samar wa kasar lambobin zinare da tagulla a gasar wasannin Afrika da duniya baki daya.A cikin wannan shirin za mu ji ko a ina aka kwana dangane da wannan tsari a Najeriya....more11minPlay
August 29, 2020Wasanni - Messi ya sha alwashin rabuwa da BarcelonaShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi nazari ne kan tsamin dangantakar da aka samu tsakanin kaftin din Barcelona Lionel Messi da shugabannin kungiyar, abinda ya sanya dan wasan shan alwashin sauya sheka zuwa wata kungiyar....more11minPlay
August 21, 2020Wasanni - Sevilla zata kara da Inter Milan a gasar EuropaA yau juma’a Inter Milan zata fafata da Sevilla a gasar cin kofin Europa a birnin Cologne na kasar Jamus da misalin karfe 7 agogon GMT, takwas kenan agogon Najerita da Nijar.Sevilla za ta yi kokarin kare martabar kungiyoyin kasar Spain, yayinda Inter Milan a nata geffen za ta nemi sake dawo da sunan Italiya sahun kasashe dake girmama kwallon kafa a Duniya....more11minPlay
August 17, 2020Wasanni - Gasar neman cin kofin zakarun Turai ta zo da mamakiShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad, ya yi nazari ne kan wasannin daf da na karshe na gasar neman cin kofin zakarun nahiyar Turai, inda kungiyoyi hudu da suka rage suka fito wato biyi a Faransa da kuma biyu a Jamus, bayan da aka sha mamaki a wasan daf da na kusa da na karshe na kungiyoyi 8....more10minPlay
August 14, 2020Wasanni - Gasar zakarun Turai a LisbonA karon farko cikin shekaru 25, PSG ta Faransa ta samu gurbi a matakin wasan dab da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta doke Atalanta da kwallaye 2-1a karawar da suka yi jiya a Lisbon.Yanzu haka PSG za ta hadu da RB Leipzig a ranar Talata mai zuwa a matakin wasan dab da na karshe na gasar.A cikin shirin za mu duba halin da ake cikin dangane da dambarwar da ta kuno kai a Jihar Maradi....more11minPlay
August 08, 2020Wasanni - Hanyoyin ceto wasannin kwallon kafa a Jamhuriyar NijarA Jamhuriyar Nijar ,ma'abuta kwallon kafa na ci gaba da kokawa biyo bayan matsalolli da suka dabai-baye Duniyar kwallon kafa musaman a jihar Maradi.A cikin wannan shirin mu samu tattaunawa da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a Duniyar kwallon kafa.Sai ku biyo mu....more11minPlay
August 03, 2020Wasanni - Muhimman abubuwan da suka faru a firimiyar banaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a gasar firimiyar Ingila da aka kammala. Sannan za ku ji fashin bakin masana game da nasarar da Arsenal ta samu ta lashe kofin FA a karo na 14....more11minPlay
July 27, 2020Wasanni - Yadda Damben zamani ke sauya salon na gargajiya da aka saba a AfirkaShirin Duniyar Wasanni a wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad, ya yi dubi dangane da Damben gargajiya ne kamar yadda aka san shi ada da kuma yadda Damben zamani musamman daga nahiyar Asia ke shafar tsari da salon gudanar sa a yanzu. Kazalika shirin ya duba yadda yanzu ake wa Damben na gargajiya haye sabanin gado watau wasan da tun farko ake dangantawa da Mahauta....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.