Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
July 20, 2020Wasanni - Dan Najeriya ya lashe babbar gasar dambe a AmurkaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan nasarar da dan Najeriyar nan, Kamaru Usman ya samu a babbar gasar damben zamani da aka gudanar a Amurka. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa dan wasan saboda bajintar da ya nuna. Kazalika shirin ya yi nazari kan kalubalen da ke gaban Real Madrid bayan ta lashe kofin La Liga karo na 34 a Spain....more11minPlay
July 13, 2020Wasanni - Nazari kan kura-kuran da na'urar VAR ke tafkawa a wasanniShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan cece-kucen da ake yi kan kura-kuran da na'urar VAR ke tafkawa a yayin taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci. A baya-bayan nan Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta amince cewa, na'urar ta yi kuskure wajen bada bugun fanariti a wasu wasannin da aka yi a makon jiya a gasar firimiyar kasar. Kazalika shirin ya yi fashin-baki kan sabon jadawalin gasar zakarun Turai a matakin kwata-fainal, inda Real Madrid ke fuskantar barazanar rasa gurbi....more10minPlay
July 10, 2020Wasanni - Tasirin rufe makarantu kan harakokin wasannin dalibai a makarantuTun bayan shelanta bullar cutar COVID 19 a duniya, hukumomi a Nigeria suka yi ta bijiro da matakai don dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma. Daga cikin matakan da aka dauka har da rufe dukkan makarantun kasar daga matakin firamari zuwa manyan makarantu, matakin da ya yi tasiri kan harakokin wasannin motsa jiki na dalibai a wadanan makarantu.Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba halin da ake ciki a kasar ta Najeriya....more11minPlay
July 06, 2020Wasanni - Yadda Real Madrid ta daura damarar lashe gasar Laliga duk da barazanar Barcelona...more11minPlay
June 19, 2020Wasanni - Wasanni bayan CoronavirusBayan dogon hutu da shirin ya tafi sakamakon annobar coronavirus wadda ta tilasta dakatar da ilahirin wasanni a Duniya, to awannan mako shirin ya dawo yadda aka saba jin sa,A karshen mako aka koma gasar La liga ta kasar Spain, gasa ta biyu mafi girma a nahiyar turai bayan gasar pirimiya, kuma hakan ne yasa shirin na wannan mako zai maida hankali kan dawowar gasar da kuma kalu balen dake tattare da kungiyoyi da kuma su kansu yan wasa, lura da dogon hutun da suka share ba tare da atisaye ba....more11minPlay
March 27, 2020Wasanni - Dalilan dage wasannin Olympics zuwa shekara ta 2021Bayan share shekaru bakwai,kasar Japan na shirin karbar bakucin wasannin Olympics na shekarar bana,hukumar CIO dake da nauyin shirya wasannin ta sanar da dage gasar zuwa shekara ta 2021 sabili da cutar Coronavirus.Matakin da wasu yan kasar ta Japan suka soma bayyana damuwa,yayinda wasau ke ganin cewa ya dace a dage wannan gangamiAbdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni,ya ji ta baki wasu daga cikin masu ruwa tsaki a Duniyar wasanni kamar dai yada zaku ji....more11minPlay
March 23, 2020Wasanni - Annobar Coronavirus ta dagula jadawalin wasanni daban dabanShirin Duniyar Wasanni na wannan lokacin ya duba yadda annobar murar Coronavirus ta haifar da tsaiko kan wasanni daban daban a fadin duniya, gami da jirkita jadawalinsu. Shirin ya tattauna da masana kan makomar sha'anin wasannin muddin aka gaza shawo kan annobar a kasa da watanni 2....more11minPlay
March 20, 2020Wasanni - Yadda cutar Coronavirus ta shafi wasanni gami da magoya bayaShirin Duniyar Wasanni na wannan lokacin yayi nazari ne kan yadda annobar murar Coronavirus da ta zamewa duniya alakakai ta hana gudanar wasanni a sassa daban daban....more11minPlay
March 16, 2020Wasanni - Karancin kayayyakin kula da lafiya a filayen wasan NajeriyaA ckin shirin 'Duniyar Wasanni' Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari kan yadda ake samun matsalar karancin kayayyakin kula da lafiya ko rashin su a filayen wasannin Najeriya....more10minPlay
March 09, 2020Wasanni - Yadda aka yi watsi da kwallon kafa a makarantun NajeriyaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi nazari ne kan yadda aka yi watsi da wasanni tsakanin daliban makarantu a Najeriya....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.