Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
March 06, 2020Wasanni - Kasaitaccen bikin gasar El-Clasico a birnin Lagos na NajeriyaShirin Duniyar wasanni na wannan makon zai mayar da hankali ne kan yadda Hukumar La Liga ta Spain ta shirya wani kasaitaccen bikin gasar El-Clasico a birnin Lagos na Najeriya, inda tsohon dan wasan Kamaru, Samuel Eto’o kuma Jakadan La Liga a Afrika ya kasance babban bako.Abdurahaman Gambo ya halarci bikin kamar dai yada zaku ji a cikin wannan shiri....more10minPlay
March 02, 2020Wasanni - Gasar kwallon kafa ta kankama a BornoShirin Duniyar Wasanni na wannan karon yayi tattaki zuwa jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram, inda a yanzu gasar kwallon kafa ta farfado da karsashinta duk da fuskantar matsalolin tsaro....more10minPlay
February 28, 2020Wasanni - Matsalolin da suka sanya dakatar da wasannin Polo a NijarA Jamhuriyar Nijar ana fuskanatar koma baya a Duniyar sukuwar dawakai a dai dai lokacin da Najeriya ke ta kokarin ganin an samu ci gaba a wannan sashe.Wasu daga cikin jihohin Jamhuriyar Nijar da aka samu koma baya dangane da sukuwar dawakai sun hada da birnin Yameh, Maradi, Zinder.Abdoulaye Issa ya duba mana halin da ake ciki yanzu haka a cikin shirin Duniyar wasanni....more11minPlay
February 24, 2020Wasanni - Nazari kan yadda Najeriya ta yi watsi da tsarin zakulo 'yan wasaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Ahmad Alhassan ya tattauna ne yadda Najeriya ta yi watsi da tsarin zakulo matasan 'yan wasa daga sassan kasar domin wakiltar ta a gasa daban daban na Afrika da duniya....more11minPlay
February 17, 2020Wasanni - Sabon jadawalin hukumar FIFA kan mizanin kwarewar kasashe a fagen kwalloShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi nazari kan Jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke fitarwa kan matakin kwarewar tawagogin kwallon kafar kasashe....more10minPlay
February 14, 2020Wasanni - Halin da wasan kwallon kafa ke ciki a jihar AgadesShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi tattaki ne zuwa jihar Agadez dake Jamhuriyar Nijar, inda ya duba halin da wasannin kwallon kafa ke ciki....more11minPlay
February 10, 2020Wasanni - 'Yan Kenya sun lashe gasar Marathon ta LagosShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Ahmed Abba ya tattauna ne kan gasar gudun yada-da-kanin-wani da aka fi sani da Marathon da aka gudanar a jihar Lagos ta Najeriya, inda dubban 'yan wasa daga kasashen duniya daban-daban suka halarta. 'Yan Kenya ne suka lashe gasar a bangaren maza da mata,...more10minPlay
February 07, 2020Wasanni - Fifa na fatan hukumar CAF ta canza lokuta na shirya gasar AfrikaA taron birnin Rabat na kasar Morocco da ya hada hukumar Fifa da ta Caf,Gianni Infantino Shugaban hukumar Fifa ya bukaci hukumar Caf da ta yi nazari tareda dage gasar cin kofin nahiyar Afrika kama daga shekaru biyu zuwa hudu.Shawarar shugaban ta Fifa na zuwa ne a wani lokaci da kwallon kafa a Afrika ke fama da matsalolli.Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba halin da ake ciki kamar dai yadda za a ji....more11minPlay
February 03, 2020Wasanni - Yadda kasuwar musayar 'yan kwallon kafa ta kaya a TuraiShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci ya maida hankali kan yadda kasuwar musayar 'yan kwallon kafa ta kaya a Turai cikin watan Janairun da ya gabata, wadda wasu ke ganin bata yi armashi kamar yadda akayi zato ba....more10minPlay
January 27, 2020Wasanni - Me yasa Dangote ke son sayen Arsenal a maimakon Kano Pillars?Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne game da kudirin Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote na sayen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila. Wasu masharhanta na ganin cewa, bai kamata Attajirin ya karkata hankalinsa kan Arsenal ba, lura da cewa akwai dimbin kungiyoyin kwallon kafa irinsu Kano Pillars a Najeriya da ya kamata ya fara saya. Kuna iya latsa kan hoton labarin domin sauraren cikakken shirin da kuma tsokacin da Dangote ya yi mana....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.