Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
July 15, 2019Wasanni - Sharhin wasannin kusa da karshe na gasar cin kofin AfrikaShirin Duniyar Wasanni na wannan karon ya mayar da hankali ne kan wasannin daf da na karshe da aka buga aci gaba da gasar neman cin kofin nahiyar Afrika da ke gudana a kasar Masar. Shirin ya kuma tabo batun fasahar nan mai ganin kwakwaf wadda ke taimakawa alkalan wasa, VAR, wadda wasu ke korafi a kanta....more10minPlay
July 12, 2019Wasanni - Najeriya,Tunisia,algeria da Senegal sun samu tsallakawa mataki na gaba a MasarShirin namu na yau zai mayar da hankali ne zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afrika dake gudana a Masar.Ta tabbata kungiyoyi hudu ne yanzu suka samu damar tsallakawa zuwa mataki na gaba, kungiyoyin da suka hada da Najeriya,Senegal, Tunisia da Algeriya.Abdoulaye Issa ya duba mana halin da ake ciki yanzu haka....more11minPlay
July 08, 2019Wasanni - Lamurran bazata sun auku a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta banaShirin Duniyar wasanni na wannan makon, yayi nazari kan gasar cin kofin duniya da Amurka ta yi nasarar lashewa a Faransa, sai kuma yadda al'amuran bazata ke aukuwa a gasar cin kofin nahiyar Afrika AFCON, da ke gudana a kasar Masar....more10minPlay
July 05, 2019Wasanni - Amurka zata kara da Netherlands a gasar cin kofin Duniya na mata a LyonA cikin shirin Dunbiyar wasanni ,zaku ji ko a ina aka kwana dangane da shirin da yan wasan Amurka mata ke yi don karawa da kungiyar kwallon kafar Netherlands a gasar cin kofin Duniya na mata dake gudana a Faransa.Ranar lahadi 7 ga watan yuli ne yan wasan Amurka zasu kara da kungiyar kwallon kafar Netherlands a Lyon dake kasar Faransa,a cikin shirin Abdoulaye Issa ya mayar da hankali tareda samun tattaunawa da masana kwallon kafa dangane da ci gaban da aka samu a duniyar kwallon kafa bangaren mata....more11minPlay
July 01, 2019Wasanni - Yadda kungiyoyin kasashen Afrika ke ba da mamaki a gasar cin kofin Nahiyar a MasarShirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan yadda gasar cin kofin Afrika ke ci gaba da gudana can a Masar....more11minPlay
June 28, 2019Wasanni - Kungiyoyin Afrika ba su gamsu da na'urar VAR a gasar cin kofin Duniya na mataKasashe da dama ne suka yi tir da Allah wadai zuwa hukumar Fifa dangane da wannan na’urar bidiyo ta VAR da aaka yi amfani da ita a lokacin gasar cin kofin Duniya ta mata dake ci gaba da gudanaa Faransa.Tsokaci dake zuwa biyo bayan kawar da kungiyoyin mata na kasashen Afrika.Cikin shirin Duniyar wasanni,zaku ji ko a in aka kwana dangane da gasar cin kofin Nahiyar Afrika a Masar....more11minPlay
June 26, 2019Wasanni - Kasashen da za su iya lashe gasar kofin AfrikaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan kasashen da za su iya lashe gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Masar. Masana kwallon kafa a Afrika irinsu Kanu Nwanko da Daniel Amokachi da Garba Lawan sun shaida wa RFI Hausa hasahensu game da gasar. Kuna iya latsa kan hoton domin sauraren cikakken shirin....more11minPlay
June 21, 2019Wasanni - Kasashe 24 na fafatawa a gasar cin kofin Afrika a MasarShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna ne game da gasar cin kofin kasashen Afrika da ake fara gudanarwa a wannan Juma'a a kasar Masar....more11minPlay
June 17, 2019Wasanni - An kaddamar da gasar HIFL tsakanin jami'o'in NajeriyaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da gasar kwallon kafa ta jami'o'in Najeriya da za a fara gudanarwa a ranar 18 ga watan Yunin 2019, inda jami'o'i 32 za su fafata da juna, yayinda za a shafe tsawon makwanni 21 kafin kammala gasar baki daya. Kuna iya latsa hoton labarin domin sauraren cikakken shirin....more11minPlay
June 14, 2019Wasanni - Rawar da mata ke akawa a Duniyar Kwallon kafaA cikin shirin Duniyar wasanni,mun samu tattaunawa da wasu mata dake sha'awar kwallon kafa,mutanen da suka bamu nasu sani dangane da gasar cin kofin Duniya ta kwallon kafa dake gudana a Faransa yanzu haka.A cikin shirin mun nemi ji ta bakin Abdoulaye Hassane da ya taba rike mukamin shugabancin hukumar kokowa a Nijar ,wanda ya mana nazari a kai....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.