Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 591 episodes available.
April 15, 2019Wasanni - Jadawalin kasashen da za su kara a gasar cin kofin AfrikaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne game da jadawalin kasashen da za su fafata da juna a Gasar Cin Kofin Kasashen Afrika da kasar Masar za ta karbi bakwanci daga ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli. A karon farko kenan da kasashe 24 ke karawa a wannan babbar Gasar Kwallon Kafa a nahiyar. Wasu masana na ganin cewa, sabbin kasashen da suka shiga gasar a bana za su iya bada mamaki....more11minPlay
April 05, 2019Wasanni - Shugaban hukumar Fenifoot ya ziyarcin wasu jihohin NijarShugaban hukumar kwallon kafar Jamhuroyar Nijar Kanal Djibrilla Hamidou ya ziyarci wasu jihohin kasar domin ganewa idanun sa ci gaban da aka samu ta bangaren kwallon kafa ,banda haka Kanal Hamidou da sunan hukumar Feniffot ya taimakawa kungiyoyi na cikin gida da kayakin kwallo,kamar dai yada zaku ji a cikin shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa ....more11minPlay
April 01, 2019Wasanni - Wasan karshe na gasar Fives a KadunaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Ahmed Abba ya tattauna ne akan gasar Fives da aka fi sani da kwallon Sardauna da aka gudanar tsakanin jihohi a birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya....more10minPlay
March 25, 2019Wasanni - Kasashen Afrika sun kammala wasannin neman cancantar zuwa gasar AFCONShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya tattauna kan wasannin neman cancantar halartar gasar cin kofin kwallon kafa ta Nahiyar Afrika, wadda aka gama a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, 2019....more10minPlay
March 22, 2019Wasanni - Fifa na nazarin yiyuwar kara yawan kasashen da ke shiga gasar kofin duniyaYanzu haka hukumar kwallo kafa ta duniya FIFA ta fara nazarin yiyuwar kara yawan kasashen da za su shiga gasar neman kofin duniya. Shugaban hukumar Gianni Infantino ne ya sanar da wannan aniya.A cikin shirin Duniyar Wasanni na wannan mako, Ahmed Abba ya yi dubi a game da wannan yunkuri....more10minPlay
March 18, 2019Wasanni - Tsokacin masana kan Gasar Zakarun Turai zagayen Kwata FinalShirin Duniyar Wasanni a wannan karon yayi tsokaci kan yadda fafatawar kungiyoyi za ta kaya a matakin zagayen kwata final, da kuma kungiyoyin da za su yi nasarar kaiwa mataki na gaba....more11minPlay
March 04, 2019Wasanni - Yadda rauni ke dakile yunkurin ‘yan wasa na kafa tarihi a duniyar kwalloShirin na wannan makon da AbduRahman Gambo Ahmad ya jagoranta, ya dora ne akan na makon jiya, wanda yayi nazari kan yadda masu horar da kwallon kafa ke fuskantar kalubale, da kuma yadda matsalar rauni ke kashe yunkurin ‘yan wasa na kafa tarihi a duniyar tamaula.Shirin ya kuma tuntubi masana kan yadda Barcelona ke lallasa Real Madrid a yanzu....more11minPlay
February 25, 2019Wasanni - Dalilan da ke haddasa koma baya ga masu horar da kungiyoyiShirin Duniyar Wasanni da AbduRahman Gambo Ahmad ya gabatar, yayi nazari kan wasu daga cikin dalilan da ke haddasawa masu horar da kungiyoyin kwallon kafa fuskantar koma baya. Zalika shirin ya yi tsokaci kan matsalar samun raunuka da ke yawaita tsakanin yan wasan kwallon kafa....more11minPlay
February 22, 2019Wasanni - Bikin tarbar 'yan wasan Mali da suka lashe gasar AFCON a NijarShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci da Abdullahi Isa ya gabatar, yayi tattaki zuwa kasar Mali, inda akayi bikin tarbar tawagar kwallon kafa ta 'yan wasan kasar, 'yan kasa da shekaru 20 da suka lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika....more11minPlay
February 18, 2019Wasanni - Mali ta lashe Gasar Afrika ta Matasa a NijarShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Ahmed Abba ya tattauna ne game da nasarar da Mali ta samu wajen lashe Gasar Cin Kofin Afrika ta Matasa 'Yan kasa da Shekaru 20 da aka gudanar a Jamhuriyar Nijar....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 591 episodes available.