Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
December 10, 2018Wasanni - Taron karrama bikin 'yan wasan Najeriya daga fannoni daban-daban a jihar KanoShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci yayi nazari karon wani taron karrama 'yan wasan Najeriya da suka yi fice a fannonin wasannin da suke yi daban-daban.Shirin ya tattauna kan dalilin shirya taron irinsa na farko, da wasu batutuwa da ke zama kalubale ga al'amuran wasanni....more11minPlay
December 07, 2018Martanin kasashen Afrika ga hukumar CAFA yau juma'a shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ,Ahmad Ahmad zai tattaunawa da sashen faransanci na rediyon Faransa RFI, da niyar kawo karin haske dangane da matakin da hukumar ta dau na canza kasar da zata karbi bakuncin gasar cin kofin Afrika na Shekara ta 2019.A cikin shirin Duniyar Wasanni,Abdoulaye Issa ya samu tattaunawa da masu sharhi dangane da batutuwan da suka jibanci kwallon kafa a Afrika....more11minPlay
December 03, 2018Wasanni - Martanin 'Yan Kamaru dangane da kwacewa kasar damar karbar bakuncin gasar AFCONShirin Duniyar Wasanni na wannan lokacin, ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki akan harkar wasanni dangane da matakin hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF na kwace damar da ta baiwa kasar Kamaru ta karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika da aka shirya za ta gudana a shekarar 2019....more11minPlay
November 30, 2018Wasanni - Rikicin Shugabancin a kungiyoyin kwallon kafa a NijarYanayin shugabancin kungiyoyin kwallon kafa a Nijar ya soma haifar da jan kafa ga rayuwar kungiyoyin a cikin jihohin kasar.Masu sharhi sun mayar da hankali tareda gabatar da shawarwari da za su taimaka domin ingantan bangaren kwallon kafa a Nijar.Shirin duniyar wasanni tareda ni Abdoulaye Issa...more11minPlay
November 26, 2018Wasanni - Birnin Abuja zai karbi bakuncin kakar wasannin motsa jiki na NajeriyaShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci wanda AbduRahman Gambo Ahmad ya shirya ya kuma gabatar, ya tattauna akan shirye-shiryen gudanar da kakar wasannin motsa jiki na Najeriya, wanda babban birnin kasar Abuja zai karbi jagoranci.Za a soma wasannin daga ranar 6 ga watan Disamba na wannan shekara zuwa ranar 16 ga watan....more11minPlay
November 23, 2018Wasanni - Didier Drogba yayi ritaya daga Kwallon kafaDidier Drogba dan kasar Cote D’Ivoire dake taka leda a baya a kulob na Phoenix dake kasar Amurka ya sanar da yi ritaya daga kwallon kafa.Didier Drogba da ya taba taka leda a Chelsea na kasar Ingila, dan wasan mai shekaru 40 ya jeffa kwallaye 164 a wasanni 381 da ya bugawa Chelsea, yayinda ya lashe kofin firimiyar ingila Ingila sau hudu da kofin FA hudu da kuma kofin gasar zakarun Turai a shekarar 2012.A cikin Shirin duniyar Wasanni za mu duba irin rawar da ya taka a harakokin wasannin kwallon kafa....more11minPlay
November 19, 2018Wasanni - Najeriya ta samu gurbi a Gasar Cin Kofin Afrika a KamaruShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan nasarar da kasashen Najeriya da Morocco da Mali da Uganda suka samu ta samun gurbi a Gasar Cin Kofin Afrika da kasar Kamaru za ta karbi bakwanci a shekarar 2019....more11minPlay
November 16, 2018Wasanni - AS SONIDEP ya lashe kofin gasar Ligue a NijarShirin na yau zai kai mu ne a Jamhuriyar Nijar tareda mayar da hankali zuwa ga nasarar da kulob na AS SONIDEP dake birnin Yameh ya samu tareda lashe kofin gasar Ligue da ake gudanarwa kowace shekara a fagen kwallon kafa a Nijar.Shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa ....more11minPlay
November 12, 2018Wasanni - Wasanni na hada kan al'umma masamman matasaShirin duniyar wasannin na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu, ya tattauna ne kan matakin gwamnatin Najeriya na sake farfado da bukin wasanni na kasa wanda akeyi tun 1973, wanda tsohon shugaban kasar Yakubu Gawan ya samar, matakin da gwamnatin tace hanya ce da ke hada kawunan al’umma masamman matasa....more10minPlay
November 05, 2018Wasanni - Matsalar da ta hana Kano Pillars lashe kofin Aiteo a NajeriyaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne game da matsalar da ta haddasa kashin da Kano Pillars ta sha a hannun Enugu Rangers a wasan karshe na gasar cin kofin kalubale ko kuma Aiteo Cup a Najeriya. Kano Pillars ce ta fara zura kwallaye uku, sannan ta ci gaba da jan ragama har fiye da minti 70. Sai dai abin mamaki, cikin kasa da minti 20 Enugu Rangers ta farke dukkanin kwallayen uku kafin daga bisani ta kuma doke Pillars a bugun fanariti da ci 4-2. Ana kallon wannan nasarar tamkar al'mara, yayin da Pillars din ta kori daukacin 'yan wasanta har sai ta neme su nan gana a cewarta....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.