Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
September 10, 2018Wasanni - NFF ta dakatar da gasar firimiyar NajeriyaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da matakin da Hukumar Shirya Gasar Lig ta kasar da tauka na dakatar da gasar a bana tare da mika kofi ga kungiyar Lobi Stars duk da cewa ba a kammala gasar ba, matakin da masharhanta ke cewa zai yi mummunan tasiri a tsarin shirya gasar. Kazalika shirin ya tattauna kan matakin dakatar da kocin Super Eagles Salisu Yusuf har na tsawon shekara guda tare da cin sa tarar Dala dubu 5 kan samun sa da karbar cin hancin dubu 5....more11minPlay
September 07, 2018Wasanni - 'Yan wasan Benin sun yi cogen shekaruShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdoulaye Isa ya tattauna ne game da cogen shekaru tsakanin 'yan wasan Benin 'yan kasa da shekaru 17, abin da ya sa aka kama su a Jamhuriyar Nijar....more11minPlay
September 03, 2018Wasanni - Sharhi kan jadawalin gasar zakarun TuraiShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi sharhi ne kan rukunai mafi wahala a jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai ta bana. Kazalika a karon farko kenan cikin shekaru 9 da Real Madrid za ta fafata a gasar ba tare da gwarzon dan kwallon duniya ba, wato Christiano Ronaldo da ya koma Juventus. Har ila yau shirin ya yi nazari kan kalubalen da ke gaban Manchester United da kuma cece-kucen da ake yi kan yadda aka bai wa Luca Modric kyautar gwarzon dan kwallon nahiyar Turai....more11minPlay
August 31, 2018Wasanni - Makomar kungiyar Super Falcons ta NajeriyaA cikin shirin Duniyar wasanni, za ku ji halin da kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Falcons ke ciki yan lokuta bayan da ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Duniya na mata.Yan matan na Najeriya sun dawo gida ba tareda sun samu nasara a gasar cin kofin Duniya na shekara ta 2018.Shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa....more10minPlay
August 20, 2018Wasanni - FIFA, ta bukaci maida Amadu Finik kan mukaminsa ko ta haifarwa kwallon Najeriya tarnakiShirin duniyar wasanni na wannan mako, da Ahmed Abba ya gabatar, ya yi nazari ne kan umarnin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta baiwa mahukumtan Najeriya, na mayar da shugaban hukumar kwallon kafar kasar Amaju pinnick kan mukaminsa, ko kuma su fuskanci fushinta....more10minPlay
August 17, 2018Wasanni - Gasar League Pro a Jamhuriyar NijarA Jamhuriyar Nijar ,hukumar kwallon kafar kasar ta bulo da wani sabon tsari da ya shafi kungiyoyin kwallon kafar kasar dake a mataki na farko,tareda shirya gasar League Pro a cikin kasar.A cikin shirin Duniyar wasanni,za mu je jihar Damagaram ko Zinder a Jamhuriyar Nijar ,masu ruwa da tsaki a duniyar kwallon kafa sun mayar da hankali tareda yi dubi dangane da muhimanci gasar ta League Pro....more11minPlay
August 13, 2018Wasanni - Nazari kan yadda kasuwar cinikin 'yan wasa ta kaya a banaShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon da AbduRahman Gambo Ahmad ke gabatarwa, yayi nazari ne akan yadda kasuwar cinikin 'yan wasa tsakanin kungiyoyin nahiyar turai ta kaya, sai kuma hasashen masana kan kungiyoyin da zasu kai ga gaci a kakar wasa ta bana....more11minPlay
August 06, 2018Wasanni - Shirye-shiryen gasar Lig-lig na kasasheShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Ahmed Abba ya yi nazari ne game da gasar Lig-Lig na kasashe da daban daban, in da a bana, manazarta ke ganin cewa, gasar firimiya lig ta Ingila za ta yi zafi sosai lura da irin zaratan 'yan wasan da ake cefanen su....more11minPlay
July 30, 2018Wasanni - Nazari kan sabbin fuskokin da suka bayyana a gasar cin kofin duniya ta 2018Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan lokaci, wanda AbduRahman Gambo Ahmad ya gabatar, ya tattauna da masana harkar wasannin kwallon kafa dangane da abubuwan ba zata da suka auku a gasar cin kofin duniya ta 2018, da aka kammala a Rasha.Shirin ya kuma tattauna kan wasu kura-kuran da aka samu yayin gudanar da gasar cin kofin duniyar....more11minPlay
July 27, 2018Wasanni - Hukumar FIFA ta yi gargadin dakatar da Najeriya daga harkokin wasanniShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan lokaci, ya tattauna kan rikicin shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF, wanda aka shafe tsawon lokaci ana takaddama akai. Tuni dai hukumar FIFA ta yi gargadin ladabtar da Najeriya, muddin ta gaza kawo karshen rikicin....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.