Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
June 08, 2018Wasanni - Hukumar Fifa ta shirya kyaututuka zuwa kungiyoyin kwallon kafa a gasar cin kofin Duniya na RashaA cikin shirin Duniyar Wasanni,Abdoulaye Issa ya duba shirin da hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa ta yi zuwa ga kungiyoyin kwallon kafa da suka samu tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya na Rasha shekarar 2018.A wannan karo hukumar Fifa kawo sauyi a shirin tareda samun karin kusan kashi 12 cikin dari na kudin da aka saba warewa....more11minPlay
June 01, 2018Wasanni - Zinedine Zidane ya ajiye aikin mai horar da kungiyar Real Madrid a SpainKwanuki biyar da lashe kofin zakarun Turai, Zinedine Zidane ya sanar da ajiye mukamin mai horar da kungiyar Real Madrid.Sanarwar da yanzu haka da dama suka soma nuna rashin gamsuwar su.Zidane bafaranshe mai shekaru 45, bai bayyana ko zai ci gaba da aikin horar da kungiyoyin kwallon kafa nan gaba ba.A cikin shirin Duniyar Wasanni Abdoulaye Issa ya dubo halind ake ciki bayan ficewar sa da kungiyar Real Madrid....more11minPlay
May 28, 2018Wasanni - Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai karo na uku a jereShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan wasan karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, in da Real Madrid ta sake kare kambinta bayan ta casa Liverpool da kwallaye 3-1. Sai dai wasan ya zo da kura-kurai da suka hada da raunin da Sergio Ramos ya yi wa Mohamed Salah, abin da wasu ke cewa da gangan ya aikata haka don hana dan wasan tabuka wani abu a wasan....more10minPlay
May 21, 2018Wasanni - Kasashen duniya sun shirya wa gasar cin kofin duniyaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahaman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan shirye-shiryen kasashen duniya game da gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci nan da kwanaki kalilan masu zuwa. Najeriya na daga cikin kasashen da tuni suka sanar da 'yan wasan da za su wakilce su a gasar. Shirin ya kuma tattauna kan irin rawar da mai tsaren ragar Italiya da kungiyar Juventus, Gianlugi Buffon ya taka a fagen tamaula a duniya bayan ya sanar da rataye takalmansa a makon jiya a Juventus....more10minPlay
May 18, 2018Wasanni - Gudanar da kwallon kafa cikin watan Ramadana a NijarA cikin shirin Duniyar wasannin,Abdoulaye Issa ya dubo halin da ake cikin musaman ko zai yiyu a gudanar da kwallon kafa a Nijar cikin watan Ramadana,Mu jiyo ta bakin wasu masu lura da lamuran kwallon kafa a Nijar....more11minPlay
May 14, 2018Wasanni - Rawar da Wenger ya taka a tsawon shekaru 22 a ArsenalShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan wasu muhimman batutuwa uku a duniyar tamaula da suka hada da kawo karshen aikin Arsene Wenger a matsayin kocin Arsenal a cikin tsawon shekaru 22 da kuma batun fafutukar kasashen da ke neman izinin daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta 2026. Sai kuma matakin da hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta dauka na ladabtar da Rasha saboda kalaman nuna wariyar launin fata akan wasu 'yan wasa bakaken fata....more11minPlay
May 11, 2018Wasanni - Hukumar Fenifoot zata samar da gidaje zuwa kungiyoyin Ligue a NijarA jamhuriyar Nijar hukumar kwallon kafa ta Fenifoot ta aiwatar da sabon tsari na samar da gidaje a matsayin Ofis zuwa kungiyoyin Ligue na kasar.Sanarwa daga Shugaban hukumar Fenifoot Kanal Djibrilla Hima a wata ziyara da ya kai Maradi tareda ganawa da masu ruwa da tsaki a harakokin kwallon kafa na yankin.A cikin shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa za ku ji irin ci gaba da aka samu a bangaren kwallon kafa dama shirin da hukumomin ke yi wajen karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika na yan kasa da shekaru 20....more10minPlay
May 07, 2018Wasanni - Kalubalen da ke gaban Najeriya yayin shirin tunkarar gasar cin kofin duniyaShirin na wannan karon yayi tsokaci akan shirye-shiryen da 'yan wasa da ma kasashe ke yi na tunkarar gasar cikin kofin duniya da za a yi a kasar Rasha cikin wannan shekara. Kasancewar Najeriya na daga cikin kasashen da zasu halarci wannan gasa, shirin na Duniyar Wasanni, ya tattauna da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafar kasar akan kalubalen da za a fuskanta da kuma hanyoyin magance su....more10minPlay
April 30, 2018Wasanni - Kwallon Dodge a NajeriyaA cikin shirin Duniyar Wasanni,Abdurrahman Gambo Ahmad ya dubo ta yadda wasu jihohin Najeriya suka soma maida hankali zuwa kwallon Dodge ko kwallon yar zulle .Kwallon Dodge ta soma samu karbuwa daga matasan Najeriya musaman arewacin kasar kamar dai yadda zaku ji a cikin shirin Duniyar Wasanni....more11minPlay
April 27, 2018Wasanni - Matsalolin gasar Lig ta Jamhuriyar NijarShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna ne kan gasar Lig ta Jamhuriyar Nijra tare da yin nazari kan wasu matsaloli da ke addabar gasar a bana....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.