Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
April 23, 2018Wasanni - Wasan Ayo na samun karbuwa a Arewacin NajeriyaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo ya tattauna ne game da wasan Ayo ko kuma Dara da Hausawa suka aro daga wasu kabilun kudancin Najeriya. Masana na cewa har yanzu da dama daga cikin jama'a ba su da cikakkiyar masaniya kan yadda wasan na gargajiya ke gudana....more11minPlay
April 20, 2018Wasanni - Sabon tsarin da zai taimakawa bangaren kwallon kafa a NijarA cikin shirin duniyar wasanni na yau juma'a ,Abdoulaye Issa ya duba yanayin tafiyar da kwallon kafa bangaren Ligue Airtel,sabon tsarin da magabatan kwallon kafa a kasar suka bulo da shi,a daya geffen akwai matsallar da ta shafi alkalanci....more11minPlay
April 16, 2018Wasanni - Ko wacce kungiya ce za ta kai labari a gasar zakarun Turai?Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da kungiyoyi hudu da za su fafata da juna a matakin wasan dab da na karshe a gasar zakarun nahiyar Turai, in da Real Madrid za ta kece raini da Bayern Munich, yayin da Liverpool za ta kai ruwa rana da Roma. Sai dai masharhanta na ganin cewa, mawuyaci ne Real Madrid mai rike da kambi ba ta fafata da Liverpool a wasan karshe ba. Masu iya magana na cewa, ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare....more11minPlay
April 13, 2018Wasanni - Sabon tsarin da zai taimakawa yan kokowa a NijarA cikin shirin Duniyar wasanni daga sashen hausa na rediyon Faransa Rfi,mun nemi jin ta bakin wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a duniyar kokowar galgajiya, tareda duba wasu daga cikin matsallolin da yan kokowa suke fuskanta bayan wasannin kasa.Shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa....more11minPlay
April 09, 2018Wasanni - Plateau United na fuskantar kalubale a gasar CAFShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan gasar cin kofin kalubale ta hukumar kwallon kafar Afrika, wato CAF da ake ci gaba da gudanarwa a biranen Afrika. Shirin ya yi nazari na musamman game da irin kalubalen da ke gaban 'yan wasan Plateau United duk da cewa ta doke takwararta ta USM Algier ta Algaria da ci 2-1 a karawar da suka yi zagayen farko a filin wasa na garin Agege da ke jihar Lagos a Najeriya....more11minPlay
April 06, 2018Wasanni - An bude wasannin kasashen renon Ingila a AustraliaTun a ranar 4 ga watan Maris ne aka bude wasannin kasashen dake amfani da harshen turanci ko Ingilishi a kasar Australiya, cikin shirin Duniyar Wasanni,mu sake dubo wasu daga cikin matsallolin da alkalan dake da nauyi alkalancin wasannin kamar yadda Fifa ta fitar da jadawalin.Banda haka za ku ji hiar da muka yi da wasu ma'abuta kwallon kafa dangane da gasar cin kofin zakarun turai....more11minPlay
April 02, 2018Wasanni - Rawar Najeriya a Wasannin Kasashen Renon Ingila a AustraliaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da wasannin kasashen renon Ingila wato Commonwealth games da za a fara gudanarwa a ranar Laraba mai zuwa a Autralia. Kazalika shirin ya zanta kan nasarar da danb damben zamani na Birtaniya Anthony Joshua ya samu akan takwaransa na New Zealand, Joseph Parker a karan battar da suka yi a birnin Cardiff....more10minPlay
March 26, 2018Wasanni - Manyan kasashe sun fara nuna kansu kafin gasar kofin duniyaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne game da shirye-shiryen kasashen da za su fafata a gasar cin kofin duniya a bana a Rasha, in da tuni manyan kasashe kamar su Brazil da Argentina da Spain da Jamus suka fara nuna cewa, lallai da gaske suke a kinstsawarsu. Shirin ya kuma yi nazari kan irin rawar da ake fatan kasashen Afrika su taka a gasar ta cin kofin duniya....more11minPlay
March 23, 2018Wasanni - Gasar neman kofin zakarun Afirka a fagen Kwallon kafa na shekara ta 2018Hukumar kwallon kafa Caf ta fitar da jadawalin yadda kungiyoyi za su kara da junan su.A cikin shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa zaku ji ta yadda hukumar kwallon kafa ta tsara yadda wasannin zasu gudana....more11minPlay
March 19, 2018Wasanni - Gasar cin kofin Turai na UefaA cikin shirin Duniyar wasanni,Abdurrahman Gambo ya duba mana halin da ake ciki dangane da batun tanttance kungiyoyi a gasar cin kofin Turai na UEFA.Nazari,sharhi tareda duba irin manyan kalubale da wasu daga cikin kungiyoyin zasu fuskanta,a wannan gasa na yankin Turai...more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.