Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
January 12, 2018Wasanni - Sake fasalta tsarin kokowa a Jamhuriyar NijarBayan kawo karshen gasar kokwa karo na 37 a jihar Damagaram ko Zinder a Jamhuriyar Nijar,da dama daga cikin ma'abuta kokowa suka soma nuna damuwa tareda bukatar gani an fasalta tsarin yada ake shirya gasar a fadin kasar.Abdoulaye Issa cikin shirin Duniyar Wasanni ya duba mana halin da ake ciki....more10minPlay
January 09, 2018Wasanni - Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon AfrikaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da dan wasan Masar mai taka leda a kungiyar Liverpool ta Ingila, Mohamed Salah da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar Afrika na shekarar 2017 a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a birnin Accra na Ghana....more11minPlay
January 08, 2018Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon AfrikaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da dan wasan Masar mai taka leda a kungiyar Liverpool ta Ingila, Mohamed Salah da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar Afrika na shekarar 2017 a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a birnin Accra na Ghana....more11minPlay
January 05, 2018Wasanni - "Hare-haren ta'addanci ya shafi ci gaban wasanni a Arewa maso Gabashin Najeriya"Shirin Duniyar Wasanni na wannan lokacin, ya yi nazari kan yadda matsalolin tsaro suka yi tasiri wajen durkusar da harkokin wasanni a wasu jihohin Najeriya, musamman wadanda ke yankin Arewa maso Gabashin kasar....more11minPlay
December 18, 2017Wasanni - Bauchi: An kammala wasannin motsa jiki tsakanin ma'aikatu da hukumomin gwamnatiShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon, ya yada zango ne a jihar Bauchi don waiwaye kan yadda wasannin motsa jikin da aka shirya a tsakanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati ya gudana....more11minPlay
December 15, 2017Wasanni - Gasar Copa Lagos ta shekara 2017Kasar Spain ce ta lashe kofi gasa kwallon yashi na Copa Lagos na shekarar 2017 da ta gudana a EKO ATLANTIC city da ke Lagos.Wannan dai ne karo na farko da kungiyar kasar Spain ta lashe irin wannan kofi bayan da ta doke takwararta ta Najeriya Super Sand Eagles da ci 6 da 5....more11minPlay
December 11, 2017Wasanni - An kammala gasar share-fagen kaka a NajeriyaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da gasar share-fagen shiga kakar wasanni da aka gudanar a jihar Kano da ke Najeriya. Manyan kungiyoyin da ke buga gasar firimiya ne suka fafata da juna, in da Kano Pillars mai masaukin baki ta yi nasarar lashe kofi. Kungiyoyin sun ce, sun shiga gasar ne don kintsawa babbar gasar firimiya mai zuwa....more11minPlay
December 08, 2017Wasanni - Gasar Ligue ta Jamhuriyar NijarA yau shirin duniyar wasannin zai maida hankali ne akan sabon tsari ko gyaran fuskan da aka kawowa gasar yan rukuni na daya na kwallon kafa a Jamhuriyar Nijar.Hukumar kwallon kafa Jamhuriyar Nijar Fenifoot ta tsaida ranar 22 ga wannan wata na Disemba ne za a koma kwambala ta kasa bayan kammala kakar bara, sai dai maimakon kungiyoyi 14 kamar yadda aka saba, a wannan karo Ligue Airtel ta Nijar za ta koma 16, daga cikin kungiyoyin da suka samu hawa rukunin na farko akwai, Espoir ta Damagaram sai kuma kulob daya na Doso da zai fito bayan karawa tsakanin Tagur da Entente....more11minPlay
December 04, 2017Wasanni - Za mu lashe kofin duniya a Rasha- NFFShirin duniyar wasanni na wanna makon tare da Abdurrahma Gambo Ahmad ya tattauna ne game da jadawalin kasashen duniya 32 da za su fafata a gasar cin kofin duniya a Rasha a badi. Shirin ya tattauna da Hukumar Kwallon Kafar Najeriya wadda ta bayyana irin kintsawarta don ganin cewa ta kai ga gaci a gasar, yayin da hukumar ta NFF ta ce, a wannan karo za ta kawo kofin Najeriya....more11minPlay
November 27, 2017Wasanni - Bunkasar Damben gargajiya a NajeriyaShirin duniyar wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmed ya dubi tagomashi da bunkasar damben gargajiya a Najeriya dama nahiyar Afirka baki daya....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.