Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
September 29, 2017Koma-baya a fagen kwallon kwando a Jamhuriyar NijarShirin Duniyar Wasanni, tare da Abdoulaye Issa na wannan karo ya mayar da hankali ne a game da yadda wasan kwallon kwodo ke fuskantar matsala a Jamhuriyar Nijar....more0minPlay
September 25, 2017Kalubalen da ke tattare da wasan kwallon DawakiShirin Duniyar Wasanni na wannan makon da AbduRahman Gambo Ahmad ke gabatarwa, yayi nazari ne kan wasan kwallon Dawaki, wato Polo, kalubalen da ke tattare da ita sai kuma sauran muhimman batutuwan da suka shafi wasan....more11minPlay
September 22, 2017Ana zargin Minista Dalung da kawo cikas ga harkar wasanni a NajeriyaMinistan wasanni da yada al'adu na Najeriya Solmon Dalung ya musanta zargin da ke cewa daga lokacin da ya karbi ragamar jagorancin ma'aikatar ne kasar ta ke ci gaba da samun koma-baya a fagen wasanni.A cikin wannan shiri na Duniyar Wasanni tare da Abdoulaye Issa, ministan ya bayyana wasu daga cikin muhimman abubuwa na ci gaba da Najeriya ta sama a fagen wasanni karkashin jagorancinsa....more0minPlay
September 18, 2017An dage wasan karshe na damben gargajiya na tsaffin 'yan wasa a KadunaShirin Duniyar Wasanni na wannan lokacin ya dora ne da kawo muku abinda ke wakana a gasar damben gargajiya a Kaduna, wadda aka shirya a tsakanin tsaffin 'yan wasan, sai dai kuma yayin da ake dakon fafata wasan karshe da zai kai ga lashe kyautar motar da aka sanya, an dakatar da wasan. Za'a ji karin bayani cikin shirin, wanda AbduRahman Gambo Ahmad ya gabatar....more11minPlay
September 15, 2017Ko an samu koma baya a harkokin wasanni a Najeriya?Shirin duniyar wasanni na wannan mako tare Abdoulaye Issa ya tattauna da Ministan wasanni da matasa na Najeriya, Solomon Dalung, wanda ke kare kansa daga caccakar da ake yi ma sa na rashin kawo ci gaba a harkokin wasanni a kasar....more0minPlay
September 11, 2017Kungiyar Plateau United ta lashe kofin gasar Premier ta NajeriyaKungiyar kwallon kafa ta Plateau United daga garin Jos, ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon kafar Premier ta Najeriya, karo na farko kenan da kungiyar ta samu wannan nasara a tarihin kafuwarta. Plateau United ta samu nasarar ce bayan lallasa masu rike da kofin kakar wasan da ta gabata, wato Enugu Rangers da kwallaye 2-0 a filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos. Kan wannan shirin na wannan lokaci ya maida hankali....more0minPlay
September 04, 2017An fara gasar cin Mota tsakanin tsaffin 'yan Dambe a KadunaShirin Duniyar wasanni na wannan makon da AbduRahman Gambo Ahmad ke gabatarwa, ya maida hankali ne kan gasar cin mota sukutum, da aka kaddamar a jihar Kadunan Najeriya. A wannan karon dai an shirya gasar ce tsakanin tsaffin 'yan Damben da suka ajiya zare, amma aka sanya su komowa fagen daga....more10minPlay
September 01, 2017Wasannin nema shiga gurabun gasar cin kofin duniya na 2022Kungiyoyin kwallon kafa a kasashen duniya na ci gaba da fafatawa domin samun guraban shigar gasar neman kofin duniya na 2022 da za a yi a Rasha.A cikin wannan shiri, AbdurRahman Gambo Ahmad, ya yi mana dubi a game da yunkurin da wasu kasashe a nahiyar Afirka ke yi na shiga gasar....more11minPlay
August 28, 2017Nazari kan jadawalin Gasar Zakarun Nahiyar TuraiShirin Duniyar Wasanni na wannan makon, yayi nazari ne, tare da tattaunawa da masana wasanni kan jadawalin gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, musamman kan kungiyoyin da ake hasashen zau taka rawar gani da wadanda ke fuskantar kalubale, da kuma dalilan da suka sabbaba hakan....more11minPlay
August 25, 2017Kammala wasannin kasashe masu mu'amala da harshen Faransa karo na 8A shirin duniyar wasanni na wannan mako, Abdoulaye Issa zai ci gaba da gabatar da hirarraki ne dangane da bikin kammala wasannin kasashen masu mu'amala da harshen Faransanci karo na 8 da aka gudanar cikin watan yulin da ya gabata a birnin Abidjan na Cote d'Ivoire....more0minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.