Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.
March 05, 2018Wasanni - Garkuwan Cindo ya lashe mota a damben gargajiyaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da gasar damben gargajiya da aka gudanar a jihar Kaduna ta Najeriya, in da aka ajiye kyautar mota kirar Peugeot 406 da Garkuwan Cindo ya lashe bayan doke Autan Dan Bunza a wasan karshe. Sai dai wasan ya haddasa gardamar da ta kai ga nazarin hoton bidiyon da aka dauka don tantance gaskiya....more11minPlay
March 02, 2018Wasanni - Bikin karrama zaratan 'yan kwallon NajeriyaA cikin watan Fabarairun da ya gabata ne aka karrama tsoffin zaratan 'yan wasan kwallon kafan Najeriya da kuma wadanda ke haskawa a yanzu, a wani gagarumin biki da aka gudanar a birnin Lagos.A yau, Abubakar Isa Dandago, zai gabatar ma na da kashi na biyu na abubuwan da suka faru a lokacin wannan biki ne....more10minPlay
February 26, 2018Wasanni - Kintsawar kungiyoyin Najeriya a gasar zakarun AfrikaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da nasarar da kungiyoyin kwallon kafar Najeriya suka samu ta shiga matakin gaba a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika da suka hada da Plateu United da MFM FC da Akwa United, in da a yanzu za su fafata da takwarorinsu na kasashen Larabawa. To ko wani irin kintsawa kungiyoyin na Najeriya suka yi wa gasar? Sai a saurari cikakken shirin....more11minPlay
February 23, 2018Wasanni - Bikin karrama zaratan 'yan kwallon NajeriyaHukumar kwallon kafar Najeriya ta yi bikin karrama wasu fitattun 'yan wasan da suka taka rawa a can baya da kuma wannan zamani.An samu halartar manyan baki a wannan biki, da suka hada ministan wasannin kasar, da shugaban hukumar kwallon ta duniya da dai sauransu.Abubakar Isa Dandago, ya halarci biki, ya kuma hada mana shiri na musamman a kai....more10minPlay
February 19, 2018Wasanni - Makomar kungiyoyin Ingila a gasar zakarun TuraiShirin duniyar wasanni na wanna makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne game da makomar kungiyoyin Ingila a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da, matakin kungiyoyi 16. Shirin ya kuma yi hasashen kan Real Madrid mai rike da kambin gasar....more11minPlay
February 09, 2018Wasanni - Nazari domin sake fasalta tsarin kokowa a Jamhuriyar NijarA cikin shirin da ya gabata kun ji halin da yan kokowa suke ciki a Jamhuriyar Nijar wanda hakan ya sanya da dama daga cikin masu ruwa da tsaki a duniyar Kokowa yin kira zuwa Gwamnatin kasar.Banda haka mun duba ta yada yan Najeriya ke fata zuwa kungiyar Super Eagles dangane da gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018.Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa ....more11minPlay
February 05, 2018Wasanni - Burin matasan Najeriya da ke buga kwallon kafa a NajeriyaShirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Haruna Ibrahim Kakangi ya tattauna ne game da burin matasan Najeriya da ke buga tamaula na zuwa kasashen Turai.Shirin ya tattauna da wani matashi da hakarsa ta gaza cimma ruwa duk da cewa saura kiris ya tsallaka Turai amma ya gamu da wani akasi.To ko menene wannan akasin? Sai a saurari cikakken shirin....more10minPlay
February 02, 2018Wasanni - Kokarin yan wasan Najeriya a gasar Chan na MoroccoA cikin shirin Duniyar Wasannin ,Abdoulaye Issa ya duba irin ci gaban da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya mai buga wasa a gida ta samu a gasar Chan na Morocco bayan da ta doke Sudan,kungiyar zata kuma karawa da Morocco a gasar karshe tareda fatan lashe kofin gasar ranar Lahadi....more11minPlay
January 29, 2018Wasanni - Kasuwar musayar yan wasa a yankin TuraiA cikin Shirin Duniyar Wasanni Abdurrahman Gambo ya yo dubi ne kan tasirin kasuwar musayar yan wasa a yankin na Turai,ya kuma samu tattaunawa da masana harakokin wasannin kwallon kafa.A daya wajen ya kuma duba irin wainar da ake tuyawa a Morocco dangane da gasar cin kofin matasa dake taka leda a gida....more11minPlay
January 26, 2018Wasanni - Nazari domin sake fasalta tsarin kokowa a Jamhuriyar NijarA Jamhuriyar Nijar,ana ci gaba da nazari domin tanttance hanyoyin kawo gyara dama fasalta tsarin kokowa a kasar.Tun bayan gangami na Damagaram ko Zinder, masu ruwa da tsaki a harakar kokowa a Nijar na iya kokarin su na gani an samu tsari kokowa ta ya dace.A cikin shirin Duniyar wasanni Abdoulaye Issa ya dubo wasu daga cikin matsalollin dake hana ruwa gudu....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 580 episodes available.