Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.... more
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 351 episodes available.
October 18, 2022Amsar tambaya kan tasirin malamin Shi'a Moqtada al-Sadr ga siyasar IraqiShirin Tambaya da amsa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya amsa wasu daga cikin muhimman tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ciki har da amsar tambaya kan neman bayani game da fitaccen malamin Shi'a na kasar Iraqi da kuma tasirinsa a siyasar kasar. Ayi saurare lafiya....more21minPlay
September 10, 2022Amsar tambaya game da tasirin jagoran shi'a Moqtada Sadr ga siyasar IraqiShirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson kamar yadda ya saba a kowanne mako yakan amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko, inda a wannan karon shirin ya amsa tambaya kan tasirin da fitaccen malamin Shi'ar Iraqi Moqtada Sadr, ke da shi ga siyasar kasar da ma takaitaccen bayani kan tsohuwar tarayyar Soviet da kuma dalilin rushewarta....more21minPlay
September 03, 2022Amsar tambaya kan tasirin tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev ga DuniyaShirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya sake amsa muhimman tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ciki har da amsar tambaya kan tasirin tsohon shugaban tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev da ya mutu a farkon makon da muke bankwana da shi, mutumin da ya yi rawar gani wajen kawo karshen yakin cacar baka a Duniya da kuma baiwa kasashen da ke karkashin tarayyar ta soviet damar cin gashin kansu....more20minPlay
August 27, 2022Tambaya da Amsa: Dalilin da ke sanya manya kasashe mallakar makamai masu linzamiShirin Tambaya da amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya amsa mabanbantan tambayoyin da kuka aikowa sashen Hausa na RFI ciki har da amsar tambaya kan makami mai linzami da kuma dalilan da ke sanya kasashe mallakar nau'in makamin. Ayi saurare Lafiya....more20minPlay
August 20, 2022Tambaya da Amsa:- Muhimman yankin Taiwan ga Amurka da kuma barazanar ChinaShirin Tambaya da amsa tare da Micheal Kuduson na kokarin amsa tambayoyin da masu sauraro ke aiko mana, kuma daga cikin amsoshin tambayoyin da za mu kawo muku a yau, har da wadda ke neman karin bayani a kan tsibirin Taiwan da abin da ya sa Amurka ke kokarin kare tsibirin duk da cewa na China ne. sai a kasance tare da mu....more20minPlay
August 13, 2022Karin biyani a kan ƙasashen da rana ba ta faduwa a duniyaA cikin shirin tambaya da amsa na yau, za mu ji bayani a kan wasu kasashen duniya da rana ba ta faduwa, sai ku kasance tare da mu.Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ daga nan sashen Hausa na Radio France Internationale. Aiko da tambaya ta adireshinmu na imel a [email protected] sai mun ji ka...more20minPlay
August 06, 2022Amsar tambaya kan tsawon lokacin da ake dauka kafin tona rijiyar MaiKamar kowanne mako shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson na kawo muku amsoshin tambayoyin da muka samu daga wasu daga cikin masu sauraronmu, kuma daga cikin tambayoyin da shirin ya amsa a yau, har da wadda ke neman bayani a kan tsawon lokacin da ake dauka wajen hakar rijiyar man fetur, da kuma inda aka kwana a game da danyen man da aka ce an gano a arewacin Najeriya. Sai ku biyo mu....more20minPlay
July 30, 2022‘Tambaya Da Amsa’ daga sashen hausa na RFITambayar da muka samu daga, Usman Manika Mai Ruwa Road Funtua a jihar Katsina, ya ce me ake nufi da dokar mallakar makamai a hukumance. Me haka ke nufi, kuma wake da alhakin Sanya wannan dokar mallakar makamai dan kare kai tsakanin gwamna da jami’an tsaro?...more20minPlay
July 23, 2022Amsar tambaya kan banbancin kudin Internet na Bitcoin da kuma PiShirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micheal Kuduson na wannan makon, za ku ji banbanci da kuma inda aka hadu a tsakanin tsarin kudin intanet na Bitcoin da kuma wanda ke shirin shiga, Pi....more20minPlay
June 25, 2022Dalilan da suka dakile kokarin warware matsalar tallafin man fetur a NajeriyaKamar yadda muka saba a duk mako, shirin ‘Tambaya Da Amsa’ na kawo muku amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana....more20minPlay
FAQs about Tambaya da Amsa:How many episodes does Tambaya da Amsa have?The podcast currently has 351 episodes available.