Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 591 episodes available.
May 01, 2017Horas da matasa a harkokin wasanni a NijarShirin Duniyar wasanni ya mayar da hankali kan shirin horas da matasa a harkokin wasanni daban-daban a Jamhuriyar Nijar tare da Abdullahi Issa....more11minPlay
April 24, 2017Muhawara tsakanin magoya bayan kungiyoyin zakarun nahiyar turaiShirin Duniyar wasanni na wannan lokacin yana dauke ne da muhawara, tsakanin magoya bayan kungiyoyi guda hudu da suka samu nasarar zuwa matakin wasan kusa da na karshe, a gasar zakarun nahiyar turai. Muhawarar ta maida hankali ne kan yadda kowa ke bayar da hujjojin da yake ganin zasu bai wa kungiyarsa damar lashe kofin gasar....more11minPlay
April 21, 2017Nijar: Gwamnati ta kaddamar da shirin farfado da wasanni a makarantun sakandareShirin Duniyar wasanni a wannan karon yayi nazari ne kan matakin farfado da wasannin motsa jiki a matakarantun sakandaren gwamnati dama masu zaman kansu, da Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar da kaddamar domin dawo da al'adar da a baya take taimakawa sosai wajen bunkasa wasanni tsakanin dalibai a kasar....more10minPlay
April 17, 2017Dalilan da ke sa wasu shahararrun 'yan kwallo na komawa Amurka da ChinaMafi yawa daga cikin shahrarren 'yan wasa musamman a fagen kwallon kafa, na kulla kwantaragi domin buga wa wasu kungiyoyi da ke China ko kuma Amurka.To sai dai abin lura a nan shi ne mafi yawansu na kulla irin wannan kwantaragi ne a daidai lokacin da suka fara shiga shekarun gaf da yin ritaya daga kwallon kafa, yayin da wasu ke daukar irin wannan mataki saboda yadda taurarinsu suka fara dushewa.A cikin na wannan mako, AbdurRahman Gambo Ahmed ya yi mana dubi a game da wannan batu....more10minPlay
April 10, 2017Wasan kwallon bango a NajeriyaShirin duniyar wasanni ya yi dubi kan wasan kwallon bango da yadda yanzu matasa ke sha’awar wasan da kuma kalubalen da ake fuskanta....more11minPlay
April 03, 2017Wasan Langa a jihar Kadunan NajeriyaDa dama dai daga cikin matasa na baya-bayan nan ba su da cikakkiyar masaniya game da wasan Langa, watakila ma wasu basu ma san shi ba baki daya.Wasan Langa a jihar Kadunan Najeriya da ke arewacin Najeriya, wasan da masana ke cewa na fuskantar barazanar bacewa, saboda rashin ba shi tallafi ko kuma goyon bayan da ya dace.Abdulrahamane Gambo ya yi tattaki zuwa Kaduna a cikin shirin Duniyar Wasanni....more11minPlay
March 27, 2017kwallon tuntun ko kuma Badminton a NajeriyaShirin na makon zai tattauna ne game da yadda wasan kwallon tuntun ko kuma Badminton a Turance ke ci gaba da samun karbuwa musamman tsakanin manyan Mutane masu shekaru 70 a Najeriya, in da kuma za ku ji dalilansu na bai wa wannan wasa muhimmanci fiye da sauran wasani a duniya tareda Abdurahamane Gambo ....more11minPlay
March 20, 2017Kalubalin da ke gaban sabon shugaban CAF Ahmad AhmadA makon da ya gabata Issa Hayatou da ya shafe shekaru 29 yana shugabancin hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ya sha kaye a zaben hukumar da aka gudanar a birnin Addis Ababa na Habasha. Shugaban kwallon kafa na kasar Madagascar ne Ahmad Ahmad ya doke Hayatou da yawan kuri’u 34. Tuni dai sabon shugaban na CAF ya sha alwashin kawo sauyi a hukumar kwallon kafar ta Afrika. Abdurrahman Gambo ya duba kalubalin da ke gaban sabon shugaban a wannan shirin....more11minPlay
March 18, 2017Ana kallon kwallo har a cikin dare a MaiduguriShirin Duniyar Wasannin ya kai ziyara ne gidan kallon kwallon kafa na El Kanemi da ake nuna wasannin Lig na Turai a garin Maiduguri a Jihar Borno Najeriya da ke fama da hare haren Boko Haram. Akwai muhawara da shirin ya hada tsakanin magoya bayan kungiyoyin La Liga da Premier tare da tattaunawa da su kan samun zaman lafiya a Borno bayan fama da barazanar Boko Haram...more11minPlay
March 13, 2017Wasan zari-ruga na fuskantar kalubale a NajeriyaShirin duniyar wasanni na wannan makon ya tattauna ne game da kalubalen da wasan zari-ruga ke fuskanta a Najeriya, duk kuwa da irin namijin kokarin da 'yan wasan kasar ke yi a kasashen ketare. Abdurrahman Gambo Ahmad ya ziyarci filin wasan zari-ruga na jihar Kaduna, in da ya tattauna da 'yan wasan da suka bayyana masa irin nasarorin da suke samu a kasashen waje, amma gwamnatin kasarsu ba ta nuna halin-ko-in-kula ba, abin da suka ce yana rage musu kwarin gwiwa wajen ci gaba da kara kaimi....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 591 episodes available.