Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 231 episodes available.
November 14, 2022Rawar da kasashen Afirka za su taka a QatarShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi nazari ne game da irin rawar da ake sa ran kasashen Afrika za su taka a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Qatar....more10minPlay
November 07, 2022Yadda manyan kungiyoyi suka gaza taɓuka abin kirki a gasar zakarun Turai ta 2022Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida da hankali kan yadda manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai a bana suka gaza tabuka abin kirki a gasar zakarun Turai. A ranar Larabar da ta gabata ne aka kammala wasannin rukuni na gasar zakarun nahiyar Turai, inda aka samu kungiyoyi 16 da suka kai matakin zakaye na biyu a gasar....more10minPlay
October 31, 2022Gasar motsa jiki na dakarun kare gandunn daji a YankariShirin Duniyar Wasanni a wannan mako zayyi bitar gasar motsa-jiki na zaratan da ke kare dajin daga farauta da kiwo ko sarar itatuwa wanda ake kira da Wildlife Ranger Challenge a Turance....more10minPlay
October 24, 2022Yadda bikin bayar da kyautar gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or ya gudana a ParisShirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda bikin bayar da kyautukan gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or ya gudana a birnin Paris, kyautar da a wannan shekara dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da Real Madrid Karim Benzema ya lashe saboda rawar da ya taka wajen taimakawa kungiyarsa kai labari a mabanbantan gasa cikin kakar da ta gabata. Ayi saurare Lafiya....more10minPlay
October 17, 2022Waiwaye kan rawar da Najeriya ta taka a gasar Commonwealth a BirtaniyaShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya tattauna ne akan irin rawar da tawagar 'yan wasan Najeriya ta taka a lokacin gasar guje-guje da tsalle-tsalle na kungiyar kasashe renon kasar Ingila wato Commonwealth da aka gudanar a birnin Birmingham ta kasar Birtania....more10minPlay
October 10, 2022Hasashen kwararru kan gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a banaShirin Duniyar Wasanni na wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya tattauna da masana kan sha'anin kwallon kafa, kan yadda gasar cin kofin zakarun Nahiyar Turai ke gudana a bana....more10minPlay
October 03, 2022An zabi sabon shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya NFFShirin ya maida hankali ne kan zaben sabbin shugabannin gudanarwar hukumar kwallon kafar Najeriya wato NFF, da ya gudana makon jiya a birnin Benin na jihar Edo da ke kudancin kasar, inda aka zabi Alhaji Ibrahim Musa Gusau a matsayin sabon shugaba, bayan karewar wa’adin Mr Amaju Pinnick wanda ya kwashe tsahon zango biyu yana shugabancin hukumar....more10minPlay
September 19, 2022Yadda wasan Polo domin samar da zaman lafiya ya gudana a NasarawaShirin namu na wannan mako zai yi duba ne game da wasan dawaki wato Polo inda zai yada zango a tarayyar Najeriya....more10minPlay
September 05, 2022NFF na shirin zaben sabbin shugabannintaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da shirin Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF na gudanar da zaben domin samun sabbin shugabannin da za su jagorance ta na tsawon shekaru hudu....more11minPlay
August 22, 2022Yadda damben gargajiya ya zama hanyar samun kudi a yanzuShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh na wannan makon ya tattauna ne game da wasan damben gargajiya a Najeriya da nahiyar Afrika, inda a yanzu matasa suka rungumi harkar gadan-gadan a yanzu domin neman kudi....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 231 episodes available.