Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.
October 25, 2021Attajiran larabawa sun raja'a wajen zuba jari a fagen wasanniMasana harkar tattalin arziki na duniya sun lura cewa manyan attajiran kasashen larabawa da dama, sun fara karkatar da akalar hanyoyin samun kudin shigar su daga kan mai zuwa wasu hanyoyi na zamani, wadanda suka hada da harakokin wasanni musamman wasan kwallon kafa.Shirin Duniyar wasanni na wannan lokaci zai mayar da hankali a kai tareda Nasiru Sani....more10minPlay
October 18, 2021An fara bunkasa wasanni a Katsina don jan hankalin matasa saboda tsaroShirin 'Duniyar Wasanni' tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi leka jihar Katsina a Tarayyar Najeriya, inda mahukuntan jihar suka maida hankali don bunkasa harkokin wasannin kwallon kafa domin jan hankalin matasa da zummar kawar da hankalinsu daga fadawa miyagun laifuka da yanzu haka ke addabar jihar da wasu sassan Najeriya....more10minPlay
October 11, 2021Gwagwarmayar neman tikitin kofin duniya tsakanin kasashen AfirkaShirin 'Duniyar Wasanni' tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne a kan tawagogin kwallon kafar kasashen nahiyar Afirka da ke gwagwarmayar neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022....more11minPlay
October 08, 2021Yadda NFF ta rarrashi Isma'ila Mabo bayan ta mace shiShirin Duniyar Wasanni tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kacokan da tsohon kocin tawagar mata ta Najeriya, Isma'ila Mabo wanda Hukumar Kwallon Kafar kasar ta NFF ta rarrashe shi tare da ba shi hakuri bayan ta ki gayyatar shi zuwa wani biki da ta shirya domin karramar tsoffin 'yan wasan mata da ya horas da aka gudanar a birnin Lagos....more11minPlay
October 06, 2021Yadda NFF ta ki karrama Isma'ila Mabo (2)Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda yake tattaunawa kan rashin gayyatar tsohon kocin tawagar mata ta Najeriya Super Falcon, Isma'ila Mabo zuwa bikin karramar tsoffin 'yan wasan mata da ya horas har suka kafa gagarumin tarihi a Najeriya. Wani abu da ya zafafa cece-kuce kan lamarin shi ne yadda aka gayyato hatta matan da ke zaune a Amurka da Turai amma aka mance da Mabo wanda ke zaune a garin Jos na jihar Filato....more11minPlay
September 27, 2021Yadda NFF ta ki karrama Isma'ila Mabo (1)Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya tattauna ne kan rashin gayyatar tsohon kocin tawagar mata ta Najeriya Super Falcon, Isma'ila Mabo zuwa bikin karramar tsoffin 'yan wasan mata da ya horas har suka kafa gagarumin tarihi a Najeriya. Wani abu da ya zafafa cece-kuce kan lamarin shi ne yadda aka gayyato hatta matan da ke zaune a Amurka da Turai amma aka mance da Mabo wanda ke zaune a garin Jos na jihar Filato....more11minPlay
September 24, 2021Yadda Najeriya ta sha kashi a gasar A'isha BuhariShirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya tattauna ne game da gasar zakarun Afrika ta mata da uwargidan shugaban Najeriya A'isha Buhari ta shirya....more11minPlay
September 20, 2021Harkokin kwallon kafar Mata a jamhuriyar NijarShirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Micheal Kuduson ya duba irin ci gaba da aka samu a fannin kwallon kafar Mata a jamhuriyar Nijar, da kuma kalubalen da wannan tafiya ke da su.....more10minPlay
September 17, 2021An fara gasar kwallon kafar mata ta Aisha Buhari a LagosShirin 'Duniyar Wasanni' tare da Abdoulaye Issa ya duba gasar kwallon kafa ta mata wadda uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta dauki nauyin shiryawa, wadda ta samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a duniya har da shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino....more10minPlay
September 13, 2021Kalubalen da ke gaban kungiyoyin da ke tunkarar gasar zakarun TuraiShirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman gambo Ahmad ya mayar da hankali kan gasar zakarun Turai da kungiyoyi za su faro a gobe Talata. Gasar da yanzu haka kambunta ke hannun Chelsea bayan da ta doke Manchester City a kakar da ta gabata....more11minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.